Aregbesola Ya Nemi Yafiyar Tsohon Gwamna Da Wasu Da Ya Yi Wa Laifi, Ya Ce Sharrin Shaidan Ne

Aregbesola Ya Nemi Yafiyar Tsohon Gwamna Da Wasu Da Ya Yi Wa Laifi, Ya Ce Sharrin Shaidan Ne

  • Rauf Aregbesola ya nemi gafara a wajen tsohon gwamna Gboyega Oyetola 'ya'yan APC a jihar Osun
  • Tsohon ministan harkokin cikin gidan ya bayyana cewa yana son zaman lafiya da hadin kai ya dawo jam'iyyar APC jihar Osun kuma a shirye yake ya yi aiki don cimma haka
  • Aregbesola ya kuma nemi gafarar duk wadanda suke ganin ya yi masu ba daidai ba cikin shekaru hudu da suka gabata

Tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya nemi yafiyar tsohon gwamnan Osun, Adegboyega Oyetola da wasu da ya yi wa laifi da matakan da ya dauka cikin shekaru hudu da suka gabata.

Aregbesola wanda ya kasance gwamnan jihar Osun tsakanin 2010 da 2018, ya mika mulki ga Oyetola wanda ya yi aiki a karkashinsa a matsayin shugaban ma'aikata bayan lashe zaben gwamnan 2018.

Kara karanta wannan

An Rantsar Da Gorge Akume a Matsayin Sabon SGF, Ya Daukarwa Yan Najeriya Manyan Alkawara

Rauf Aregbesola da Adegboyega Oyetola
Aregbesola Ya Nemi Yafiyar Tsohon Gwamna Da Wasu Da Ya Yi Wa Laifi, Ya Ce Sharrin Shaidan Ne Hoto: RAUF AREGBESOLA, Adegboyega Oyetola
Asali: Facebook

Aregbesola ya ce sharrin shaidan ne

Sai dai kuma, alaka ta yi tsami tsakaninsa da Oyetola inda ya nuna adawa da zarcewarsa sannan ya caccaki dattawan jam'iyyar kan kin hukunta shi (Oyetola) saboda sauya manufofinsa da ya yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Aregbesola wanda ya isa jihar Osun bayan kammala wa'adinsa a matsayin minista karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci fadar Owa Obokun, Oba Gabriel Aromolaran da Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Olanipekun.

Bayan ne sai ya yi jawabi ga magoya bayansa a filin wasa na Nelson Mandela Freedom da ke Osogbo, babban birnin jihar.

Tsohon ministan, wanda ya yi magana cikin harshen Yarbanci ya yaba ma Buhari kan basa damar da ya yi na yi wa kasar hidima, rahoton Vanguard.

Ya kuma yaba ma shugaban kasa Bola Tinubu kan taimakon da ya yi masa a rayuwa da kuma damka masa mulki.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Gana da Shugabannin Tsaro Bayan Yan Bindiga Sun Kashe Rayuka 37, Ya Ɗauki Matakai Masu Kyau

Jaridar The Nation ta nakalto Aregbesola yana cewa:

"Ban dawo Osun don yin gaba ko nuna bangarenci ba sai don sulhunta jam'iyyarmu. Na zo nan a yau don rokon yakiyar duk wanda ke fushi da ni. Dalilin da yasa mutane ke yaba mani kan nasarorin da na samu a Osun a yau ya kasance saboda gagarumin aikin da na yi ne lokacin da nake kan mulki kuma wadanda suka mayar da kansu makiya a yau, tare muka yi aiki a gwamnati.
"Ina godiya ga Allah wanda ya dago ni daga Lagas da taimakon Shugaban kasa Bola Tinubu, shine jigon nasarata. Na shafe shekaru 8 a matsayin kwamishina a Lagas. a 2014, muka yi wata ganawa a Badagry inda muka tattauna game da yadda za mu kwato jihohinmu daga jam'iyyun adawa. Shugaban kasa Tinubu da sauran dattawan Yarbawa suka umurceni da na zo na karbe jihar Osun daga jam'iyyar adawa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Tsoffin Gwamnoni 3 Na APC da PDP, Bayanai Sun Fito

"Da taimakon Allah da taimakon Asiwaju, na yi nasarar zama Gwamna na tsawon shekaru 8 koda dai ba abu ne mai sauki ba da taimakon wadanda suka zama makiyana na shekaru hudu.
"A 2019, bayan hukuncin kotun koli, na zo wajen nan da mutumin da na mikawa mulki. Na bayyana cewa na taka rawar gani na sannan na mika mulki ga wanda nake so. Amma na ce dole ne mutum ya aikata daidai ta hanyar tabbatar da hadin kai a cikin jam’iyyar. Idan aka yi haka zan zama ubangida. Amma abin takaici, Shaidan ya sha kansu wajen yi wa abun da na fada mummunar fassara. Ban taba rokon komai daga wajensu ba lokacin da yake mulki.
"Na fadi a yau kuma ina neman yafiya. Bayan wannan, ba za mu sake rokon kowa ba kuma. Ba mu yi wa kowa laifi ba kuma ba mu yarda wani ya yi mana laifi amma ta yiwu cewa sun yarda mun yi masu laifi, wannan ne dalilin da yasa muke basu hakuri."

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Kaddamar Da Ginin Masallacin Majalisar Dokoki Na Miliyan N570

Yadda Tinubu ya kaucewa wuka mai guba yayin nada sakataren gwamnatin tarayya, Shehu Sani

A wani labari na daban, mun ji cewa Sanata Shehu Sani, ya yi shagube ga wani mai biyayya ga shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu bayan nada George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.

Tsohon sanatan na Kaduna ya bayyana cewa sabon shugaban kasar ya yi dabara da ya kaucewa wuka mai guba ta hanyar zabar tsohon kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma'aikatansa da Sanata Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel