"Yadda Tinubu Ya Kaucewa Wuka Mai Guba Da Nadin Akume": Shehu Sani Ya Yi Fallasa

"Yadda Tinubu Ya Kaucewa Wuka Mai Guba Da Nadin Akume": Shehu Sani Ya Yi Fallasa

  • Tsohon sanata, Shehu Sani, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ya yi dabara da ya tsallake wani mai biyayya gare shi ya zabi George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya
  • Dan siyasar na Kaduna ya ce da ace Tinubu ya nada 'dan bani na iya' a matsayin SGF ko shugaban ma'aikata, da ya haifar da rashin jituwa
  • Sani ya yi ikirarin cewa da dan siyasar da bai ambaci sunansa ba zai dunga daukar kansa ne kamar ya fi shugaban kasa Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima muhimmanci

Abuja - A ranar Laraba, 7 ga watan Yuni, tsohon dan majalisar tarayya daga jihar Kaduna, Shehu Sani, ya bayyana cewa Shugaban kasa Bola Tinubu "ya kaucewa wuka mai guba" ta hanyar tsallake wani mai biyayya gare shi.

A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, Sani ya ce shugaban kasa Tinubu na da wayo tunda ya nada George Akume da Femi Gbajabiamila a matsayin sakataren gwamnatin tarayya da shugaban ma'aikatan shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Jerin Nade-Nade Da Tinubu Zai Iya Yi Ba Tare Da Neman Yardar Majalisa Ba

Shugaban kasa Bola Tinubu, Geaorge Akume da Shehu Sani
"Yadda Tinubu Ya Kaucewa Wuka Mai Guba Da Nadin Akume": Shehu Sani Ya Yi Fallasa Hoto: Journalist KC, Senator Shehu Sani
Asali: Facebook

'Tinubu ya kawar da rashin jituwa', Sani

Jigon na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana cewa da shugaban kasar ya zabi wani "dan bani na iya", da ya haifar da rashin jituwa tsakanin sabon shugaban Najedriyan da mataimakinsa, Kashim Shettima.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sani ya rubuta

"Da ace Tinubu ya nada "dan bani na iya" a matsayin SGF ko shugaban ma'aikata, da ya shuka rashin jituwa tsakanin shugaban kasar da mataimakin shugaban kasa, zai dunga magana da yawo kamar ya fi su dukka biyun muhimmanci.
"Tinubu ya kaucewa wuka mai guba."

Akume ya daukarwa yan Najeriya alkawari

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa sabon sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, wanda aka rantsar a yau Laraba, 7 ga watan Yini, ya sha alwashin aiki tare da Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

An Rantsar Da Gorge Akume a Matsayin Sabon SGF, Ya Daukarwa Yan Najeriya Manyan Alkawara

Akume ya kuma yi alkawarin cewa ba zai ba yan Najeriya da Tinubu kunya ba wajen aiwatar da ayyukansa.

Har ila yau, Akume wanda ya kasance minista a karkashin gwamnatin da ta gabata na tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce zai bi sahun shugaban kasa Tinubu domin ba zai so ace ya gaza ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel