Da Dumi-Dumi: Tashin Hankali Yayin Da Aka Samu Kakakin Majalisa Guda Biyu a Jihar Nasarawa

Da Dumi-Dumi: Tashin Hankali Yayin Da Aka Samu Kakakin Majalisa Guda Biyu a Jihar Nasarawa

  • Rikicin shugabancin majalisa ya dabaibaye majalisar dokokin jihar Nasarawa kan wanda zai zama sabon kakaki
  • Rikicin neman shugabancin majalisar ya sanya ɓangarorin biyu kowanne ya zaɓi na shi kakakin majalisar daban-daban
  • Rikicin dai yana a tsakanin ƴan majalisa 11 masu goyon bayan tsohon kakakin da ƴan majalisa 13 masu goyon bayan Daniel Ogazi

Jihar Nasarawa - Rikicin shugabancin majalisar dokokin jihar Nasarawa ya ɗauki sabon salo, bayan an samu shugabannin majalisa guda biyu.

A ranar Talata ne dai rikicin shugabanci ya ɓarke a majalisar kan wanda zai zama sabon shugabanta, rahoton Leadership ya tabbatar.

An zabi kakakin majalisa 2 a jihar Nasarawa
Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta samu shugabanni biyu Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Shugabannin majalisar guda biyu da aka samar da sun haɗa da tsohon kakakin majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi da Mr Daniel Ogah Ogazi, wanda ya ke wakiltar mazaɓar Kokona ta Gabas.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sanya Labule Da Masu Neman Shugabancin Majalisa, Bayanai Sun Fito

A yayin da aka zaɓi Abdullahi a wani zama da aka yi a ministirin harkokin ƙananan hukumomi da masarautu, Ogazi ya zama kakakin majalisar a zaman da aka yi a harabar majalisar dokokin jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda rikicin ya fara

Jaridar The Nation ta rahoto cewa da misalin ƙarfe 1 na dare, ƴan majalisa 13 daga cikin 24 a ƙarƙashin jagorancin Daniel Ogazi, sun hallara a ƙofar majalisar domin shiga cikin zauren majalisar amma ƴan sanda suka hana su.

Da misalin ƙarfe 4 na asuba, sauran ƴan majalisar 11 suka iso da niyyar su yi rantsuwa amma sai suka ci karo da ƴan ɓangaren Ogazi a ƙofar shiga majalisar.

Zuwa ƙarfe 4 na yamma, ƴan majalisar 11 sun garzaya ministirin harkokin ƙananan hukumomi da masarautu a tare da jami'an tsaro inda suka zaɓi Hon Ibrahim Balarabe Abdullahi a matsayin kakakin majalisar

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mambobi Sun Zaɓi Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kogi da Mataimakinsa

Lokacin da sauran ƴan majalisar da ke a bakin ƙofar shigar majalisar suka samu labarin hakan, sai suka tsallaka ta katanga suka shiga cikin harabar majalisar amma basu samu shiga zauren majalisar ba.

Sun gudanar da rantsuwarsu inda aka zaɓi Ogazi a matsayin kakakin majalisar da Hon Mohammed Oyanki na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin mataimakinsa.

Fusatattun Matasa Sun Yi Zanga-Zanga

A baya rahoto ya zo kan yadda wasu fusatattun matasa suka gudanar da zanga-zanga a jihar Nasarawa kan shugabancin majalisar dokokin jihar.

Matasan sun yi zanga-zangar ne bayan an ɗage ƙaddamar da majalisar dokokim jihar karo na 7.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel