Mai Shekara 38 Ya Zama Shugaba Yayin da Aka Rantsar da Sababbin ‘Yan Majalisa

Mai Shekara 38 Ya Zama Shugaba Yayin da Aka Rantsar da Sababbin ‘Yan Majalisa

  • Sabon shugaban majalisar dokokin jihar Osun shi ne Adewale Egbedun ‘dan shekara kasa da 40
  • A yau ne Zababbun ‘yan majalisar da aka rantsar su ka zabi shugaba da mataimakinsa a Osun
  • Rt. Hon. Egbedun zai jagoranci majalisar, sai shi kuma Akinyode Oyewusi ya zama mataimakinsa

Osun - A jihar Osun, magana da ake yi ta ‘dan siyasar da ya zama shugaban majalisar dokoki ya na mai shekara 38 da haihuwa a Duniya.

A ranar Talata, Punch ta fitar da labari cewa Adewale Egbedun mai wakiltar mazabar Odo-Otin ya zama shugaban majalisar dokoki a Osun.

Rt. Hon. Adewale Egbedun ya dare kujerar ne bayan da Ibrahim Abiola mai wakiltar Irewole/Isokan ya tsaida shi a zaben da aka yi a yau.

Majalisa
Shugaban Majalisar Osun, Rt. Hon. Adewale Egbedun Hoto: Jimoh Ismail Adetunji Bora
Asali: Facebook

Kamar yadda rahoton ya bayyana, tsayawa takarar matashin da aka haifa a Yunin 1985 ta samu goyon bayan Honarabul Areoye Samuel.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oyewusi ya zama mataimaki

A yayin da Egbedun ya yi nasarar zama sabon shugaban majalisar, an kuma zabi Honarabul Akinyode Oyewusi a matsayin mataimaki.

Mataimakin shugaban majalisar shi ne mai wakiltar mutanen mazabar Ife ta Arewa.

Vanguard ta ce Elisha Oderinwale ne ya tsaida Oyewusi kuma nan take ya samu goyon bayan Kashope Abolarinwa mai wakiltar Ifedayo.

Kilakin majalisar dokokin, Simeon Amusan ne ya jagoranci zaman farko da aka yi bayan wa’adin majalisa ta bakwai ya kare a makon jiya.

Gwamna Ademola Adeleke

Mai girma Gwamnan Osun, Sanata Ademola Adeleke, mataimakinsa, Prince Kola Adewusi da sauran manyan gwamnati sun halarci zaman.

Babu mamaki Gwamna Ademola Adeleke yana goyon bayan Adewale Egbedun da Akinyode Oyewusi domin ya ji dadin aiki da majalisa.

Ba kasafai aka saba jin mai shekara 30 ya samu takara har ta kai ya yi nasara a zabe, kuma ya kai ga samun babban matsayi irin wannan ba.

Mulkin Bola Tinubu

An ji labari Adaku Ogbu-Aguocha ta na sa ran Shugaba Bola Tinubu zai hada-kan al’ummar kasar nan yayin da ya gaji Muhammadu Buhari.

‘Yar takarar APC a Sanatan gabashin Enugu a zaben 2023 ta ce sabon shugaban kasar ya na da kwarewar shugabanci, ya nuna haka a Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel