Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Shugaban Majalisar Dattawa da Kakaki

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Shugaban Majalisar Dattawa da Kakaki

  • Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya gana da shugabannin majalisar tarayya ta 9 masu barin gado a Aso Rock ranar Alhamis
  • Manyan shugabannin sun fara tattaunawa da misalin karfe 2 da wasu 'yan mintuna na rana bayan Tinubu ya fito zama da hafsoshin tsaro
  • Ana tsammanin taron zai maida hankali kan bikin rantsar da majalisa ta 10 wanda zai gudana ranar 5 ga watan Yuni

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya shiga ganawa yanzu haka da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila.

Jaridar Punch da rahoto cewa shugaban ya sa labule da manyan jiga-jigan 2 a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, 1 ga watan Mayu, 2023.

Tinubu, Lawan da Femi.
Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Shugaban Majalisar Dattawa da Kakaki Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Ahmad Ibrahim Lawan
Asali: Facebook

Rahoto ya nuna cewa sun shiga wannan ganawa da misalin karfe 2 da 'yan mintuna kalilan jim kaɗan bayan Sanata Lawan da Gbajabiamila sun isa Aso Rock.

Haka zalika sun shiga ganawar ne bayan shugaba Tinubu ya gana da shugabannin tsaro da Sufeta janar na rundunar yan sanda karo na farko bayan ya karɓi mulki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Menene makasudin wannan ganawa?

Duk da ba'a bayyana maƙasudin taron ba amma ana hasashen ba zai rasa alaƙa da shirin rantsar da mambobin majalisar tarayya ta 10 wanda aka tsara gudanarwa ranar 5 ga watan Yuni.

Haka zalika ana hasashen Tinubu da Lawan da Gbajabiamila zasu tattauna kan zaben sabbin shugabannni a majalisar dattawa da majalisar wakilan tarayya na 10.

Channels tv ta tattaro cewa shugaba Tinubu da APC sun tsara jadawalin shiyyar da zata samu shugaban majalisar dattawa, mataimaki, kakakin majalisar wakilai da mataimakinsa.

A rabon muƙaman majalisa ta 10, APC ta zabi Sanata Godwill Akpabio daga shiyyar Kudu maso Kudu a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Haka jam'iyya mai mulki ta miƙa kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa ga shiyyar Arewa ta Yamma inda ta ɗauki Sanata Barau Jibrin daga jihar Kano.

A ɗaya ɓangaren APC ta sake baiwa Arewa maso Yamma kujerar kakakin majalisar wakilai yayin da ta miƙa ƙujerar mataimakin kakaki ga shiyyar Kudu maso Gabas.

"Muna Cikin Mawuyacin Hali a Najeriya" Abdullahi Adamu Ya Gargadi Gwamnoni

A wani rahoton kuma Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya roki gwamnoni su tashi tsaye kuma su yi aiki a kan manufofin jam'iya mai mulki.

Sanata Adamu ya kara da cewa jam'iyyar zata baiwa kowane gwamna haɗin kan da yake buƙata kuma a shirye take ta taimaka ko da kuwa da shawarwari ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel