"Muna Cikin Mawuyacin Hali a Najeriya" Abdullahi Adamu Ya Gargadi Gwamnoni

"Muna Cikin Mawuyacin Hali a Najeriya" Abdullahi Adamu Ya Gargadi Gwamnoni

  • Shugaban APC mai mulki na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya gana da gwamnonin jam'iyyar a Abuja
  • Yayin zaman, Sanata Adamu, ya gargaɗe su da su tashi tsaye duba da mawuyacin halin da aka shiga a Najeriya
  • Ya ce duk da gwamnonin musamman sabbi sun zo a lokaci mai wahala da aka cire tallafi, ya buƙaci su dage kan manufofin APC

Abuja - Shugagan jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce Najeriya ta tsinci kanta a wani lokaci mai matuƙar wahala sakamakon cire tallafin man Fetur.

Daily Trust ta ce Adamu ya yi wannan furuci ne yayin da ya karɓi bakunci zababbun gwamnonin APC, sabbi da kuma waɗanda suka zarce a Hedkwatar jam'iyya da ke Abuja.

Abdullahi Adamu
"Muna Cikin Mawuyacin Hali a Najeriya" Abdullahi Adamu Ya Gargadi Gwamnoni Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ya kuma roƙi gwamnonin su tsaya kan manufofin jam'iyar APC mai mulkin domin ta haka ne zasu kafa shugabanci na gari ga al'ummar jihohinsu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Ɗau Zafi, Ya Ce Zai Soke Lasisin Mallakar Duk Gidan Man da Ya Ɓoye Fetur Ko Ya Kara Farashi

A kalamansa ga gwamnonin APC, Sanata Adamu ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mun shiga wani lokaci mawuyaci kuma kun zo a daidai lokaci mai wahala, cire tallafin man fetur, ba ƙaramin ƙalubale bane a gare mu, musamman ku da kuke kusa da jama'a."
"Ba abinda zamu gaya muku illa ku tsaya kai da fata a kan manufofinmu bakin gwargwado. Muna da tsarin bai ɗaya na yadda zamu shugabanci ƙasar nan kuma ku ne wakilan masu rike da tutar jam'iyya."
"A matsayinku na zabaɓɓun shugabanni a jihohinku ya zama tilas ku rungumi manufofin jam'iyyarmu, mun san akwai abubuwan da zaku fi bai wa fifiko amma ku tabbata kun taɓuka abun arziki domin cika tsammanin mutanen da suka zaɓe mu."

Zamu baku gudummuwa - Adamu

Shugaban APC na ƙasa ya kara da cewa jam'iyyar zata baiwa kowane gwamna haɗin kan da yake buƙata kuma a shirye take ta taimaka ko da kuwa da shawarwari ne.

Kara karanta wannan

"Tallafin Man Fetur Ya Tafi," Shugaba Tinubu Ya Fara Ɗaukar Matakai Masu Tsauri

Adamu ya ci gaba da faɗawa gwamnoni cewa:

"Mu a ɓangarenmu, zamu baku haɗin kan da kuke buƙata, idan kuna da matsala ku taho gare mu, zamu baku shawarwarin da ya dace. Ku sani koma ina aka je aka dawo, mai ɗaki shi ya san inda ruwa ke zuba."

Za'a Samu Jinkirin Albashi Ga Ma'aikatan FG da Jami'an Tsaro a Watan Mayu

A wani labarin na daban kuma Ma'aikatan FG da jami'an tsaro zasu fusaknci jinkiri gabannin biya su albashin watan Mayu, 2023.

Wannan dai ya samu asali ne daga jinkirin CBN na amincewa ma'aikatu su biya albashi ga ma'aikatansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel