Tinubu Bai Nada Gbajabiamila a Matsayin Shugaban Ma’aikatan Fada ba - Hadiminsa

Tinubu Bai Nada Gbajabiamila a Matsayin Shugaban Ma’aikatan Fada ba - Hadiminsa

  • Surutu ya yi yawa cewa shugaban majalisar wakilan tarayya zai yi aiki da Bola Ahmed Tinubu
  • Ana cewa Femi Gbajabiamila zai zama shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnati na Aso Rock
  • Wani na kusa da Gbajabiamila ya nuna labarin ba gaskiya ba ne, ba a ba ubangidansa mukami ba

FCT, Abuja – Rahotanni sun zagaye ko ina cewa Femi Gbajabiamila ya zama shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa a gwamnatin Bola Tinubu.

Duk yadda wannan labari ya kai ga yawo, Legit.ng ta rahoto cewa Bola Ahmed Tinubu bai yi nadin shugaban ma’akatan fadarsa ba, akalla zuwa yanzu.

Yanzu Alhamis ne, 1 ga watan Yuni 2023, babu wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriya a game da nadin mukamai, akasin abin da mutane su ke ta ji.

Gbajabiamila
Bola Tinubu da Shugaban Majalisa, Femi Gbajabiamila Hoto; @femigbaja
Asali: Twitter

Tukuna dai!

Maganar cewa Gbajabiamila ya samu mukami a fadar Aso Rock Villa kuma zai hakura da kujerarsa a majalisar wakilan tarayya ba ta tabbata ba ta tukun.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu Na Shirin Rage Alawus Din Yan Bautar Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban ma’aikatan ofishin shugaban majalisar wakilan tarayya, Olanrewaju Smart Wasiu ya yi raddi ga masu cewa Bola Tinubu ya ba uban gidansa mukami.

Da yake magana a shafinsa dazu, Olanrewaju Smart Wasiu ya bayyana labarin da ake ji da jita-jita, ya kuma yi kira ga al’umma su daina sauraron rade-radin.

Ashe labarin bogi ne

"Labaran bogi wani abin tsoro ne da ya kamata mu kawo karshensa. Ku yi watsi da jita-jitar da ake cewa labarin wani mukamin siyasa ya fito daga shafin nan.
Babu wani makamancin wannan da aka taba wallafawa a nan."

- Olanrewaju Smart Wasiu

Shugaban majalisar wakilan ya dade a majalisa, a 2023 ne ya lashe zabensa karo na shida. Tun a baya ana cewa Tinubu ya nuna Gbajabiamila zai bar majalisa.

Sai dai duk da alakar da ke tsakanin ‘dan majalisar na Surulere da sabon shugaban kasa, babu abin da ya tabbata game da ba shi kujera bayan canjin mulkin.

Kara karanta wannan

Ba a Ba Ni Mukamin Komai ba Inji Wanda Ake Cewa Ya Zama Kakakin Shugaban Kasa

Tinubu ya yi daidai - Fayose

Game da cire tallafin fetur, an j labari Ayo Fayose yana cewa ya yi imani shugaban kasa Tinubu ya dauki matakin da ya fi dacewa da tattalin arzikin kasa.

Tsohon Gwamnan ya yi kira ga 'yan Najeriya su yi hakuri da gwamnatin nan domin wahalar da aka shiga za ta tafi, ya ce gwamnatin baya ta kawo matsala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel