Gwamna Abiodun Ya Sallami Mambobin Majalisar Zartarwa, Ya Musu Kyauta

Gwamna Abiodun Ya Sallami Mambobin Majalisar Zartarwa, Ya Musu Kyauta

  • Dapo Abiodun ya rushe majalisar zartarwan jihar Ogun kwanaki kaɗan gabanin rantsar da shi a zango na biyu
  • Gwamna Abidoun ya kuma faɗa wa kwamishinoni da sauran hadimai cewa ya tsara musu kyautar rabuwa ta musamman
  • Ya ce zai sake neman wasu daga cikinsu su dawo su kara bauta wa jihar kana ya gode musu bisa nasarorin da gwamnatinsa ta samu

Ogun - Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya sallami baki ɗaya mambobin majalisar kwamishinoni da hadimansa gabanin rantsar da shi a matsayin gwamna karo na biyu.

A ranar Litinin mai zuwa, 29 ga watan Mayu, 2023, Gwamna Abiodun zai karbi rantsuwar kama aiki a zango na biyu bayan nasarar da ya samu a babban zaben 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Abiodun.
Gwamna Abiodun Ya Sallami Mambobin Majalisar Zartarwa, Ya Musu Kyauta Hoto: Prince Dr Dapo Abiodun
Asali: Facebook

Gwamna Abiodun ya sanar da korar kwamishinonin da sauran hadimansa baki ɗaya a wurin taron bankwana da mambobin majalisar zartarwa na jiha wanda ya gudana ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Kori Kwamishinoni da Hadimai, Ya Kafa Musu Sharaɗi

Abiodun ya tanadar musu ƙunshin kyauta ta musamman

A jawabinsa a wurin taron, gwamna Abiodun ya yaba wa mutanen da ya naɗa a gwamnatinsa bisa namijin kokarin da suka yi wajen yin aiki da shi don ɗaga jihar Ogun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa ya ware wasu kyaututtukan rabuwa na musamman ga kwamishinoni da sauran hadiman da zasu sauka daga kan muƙamansu.

Gwamnan ya faɗa masu cewa wannan kyauta zata iso ga kowane ɗayansu ta hannun Sakataren gwamnatin jihar nan ba da jimawa ba.

A kalamansa ya ce:

"Zan yi kewarku, amma dan Allah ina rokon mu ci gaba da gaisawa, mun cika alƙawarin da muka ɗauka, ba zai yuwu mu ci maki 100 bisa 100 saboda ba zamu iya gama komai ba."
"Amma mun yi iyakar bakin kokari kuma ina Alfahari da abubuwan da muka samu nasarar aiwatarwa tare da ku. Zamu sake kiran wasu daga cikinsu su dawo, muna fatan zaku amsa kira."

Kara karanta wannan

Gwamna Arewa Ya Kori Kwamishinoni da Hadimansa Daga Aiki, Ya Ba Su Umarni Nan Take

"Ina ƙara gode muku bisa aminta da ni da kuma yardar da kuka nuna mun muka yi aiki tare muka shugabanci jiharmu."

Ya Kamata Tinubu Ya Dau Mataki Kan Emefiele da Wasu Jiga-Jigai, Smart

A wani labarin kuma Sanatan APC ya bayyana matakan da ya kamata Bola Tinubu ya ɗauka kan waɗanda suka kawo tsarin sauya fasalin naira.

Sanata Smart Adeyemi, ya ce mutanen da basu ji ba, basu gani ba sun mutu saboda karancin takardun kuɗi a lokacin.

Ya ce wasu tilasta musu aka yi suka mutu, don haka ya nemi Tinubu ya titsiye gwamnan CBN da wasu jiga-jigai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel