Gwamnan Inuwa Yahaya Ya Sallami Mambobin Majalisar Zartarwan Gombe

Gwamnan Inuwa Yahaya Ya Sallami Mambobin Majalisar Zartarwan Gombe

  • Gwamna inuwa Yahaya na jihar Gombe ya sallami baki ɗaya mambobin majalisar zartarwa na jiharsa daga aiki
  • Ya ce ya yafe ma duk wanda mai yuwuwa ya masa laifi da sauran mutane kana ya roke su da su yafe masa
  • Kwamishinonin sun miƙa godiya ga mai girma gwamna bisa damar da ya ba su, suka ba da gudummuwa

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya rushe majalisar zartarwan jiharsa da sharadin zasu zauna a Ofis har zuwa ranar rantsuwa 29 ga watan Mayu, 2023.

Gwamna Yahaya, wanda kwanan nan ya zama shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa, ya sanar da wannan mataki ne a wurin taron bankwana da mambobin majalisar wanda ya gudana a gidan gwamnati.

Gwamna Yahaya.
Gwamnan Inuwa Yahaya Ya Sallami Mambobin Majalisar Zartarwan Gombe Hoto: Muhammad Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Ya kuma yaba musu bisa sadaukarwa, maida hankali, aiki tuƙuru da jajircewa wajen sauke nauyin da aka ɗora musu a ma'aikatun da suka jagoranta tsawon shekara huɗu.

Kara karanta wannan

Gwamna Arewa Ya Kori Kwamishinoni da Hadimansa Daga Aiki, Ya Ba Su Umarni Nan Take

Haka ya yaba musu bisa dumbin nasarorin da gwamnatinsa ta samu tsawon shekaru huɗu ta sanadiyyar gudummuwar da suka bayar a kowane irin lokaci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Yahaya ya ce wannan namijin kokari da suka jajirce a kai ne ya taimaka har jam'iyyar APC ta sake lashe zaɓe a karo na biyu, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ina rokon ku yafe mun - Gwamna Yahaya

Ya ƙara da cewa ya yafe wa duk wani mamban majalisar zartarwansa da mai yuwuwa ya masa ba daidai ba a tsawon lokacin nan, kana ya roƙi su yafe masa.

Daily Trust ta rahoto cewa a jawabinsa, Inuwa Yahaya ya ce:

"Dangane da laifin da wasunku suka mun a matsayinmu da yan adam, dama mutane ke laifi gafara kuma sai Allah, na yafe muku, ba ku kaɗai ba har sauran mutanen da suka yi kokarin ɓata mun suna."

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Tara Kwamishinoni da Hadimansa, Ya Tona Asirin Waɗanda Suka Ci Amanarsa

"Na yafe muku baki daya, sannan ina fatan kuma zaku yafe mun."

Kwamishinoni sun yaba wa Yahaya

Da suke jawabi lokuta daban-daban, kwamishinoni uku daga cikin majalisar sun yaba wa gwamna bisa damar da ya basu har suka ba da irin tasu gudummuwar wajen ci gaban Gombe.

Kwamishinonin da suka faɗi haka sun haɗa da kwamishinan shari'a kuma Antoni janar na jiha, Zubair Umar, kwamishinan yaɗa labarai da al'adu, Meshack Lauco, da kwamishinar ilimi, Aishatu Maigari.

Ranar bikin rantsarwa

A wani labarin kuma mun haɗa muku Muhimman Abubuwa 5 da Mutane Zasu Gani Ranar Bikin Rantsar da Tinubu a Abuja.

Gabannin bikin rantsar da zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ake ta jira, za a gudanar da harkoki da dama a wannan rana da ma kafin ranar.

Akwai wasu muhimman abubuwa da zasu iya faruwa a wannan ranar musamman ga mazauna birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel