Gwamna Zulum Ya Rushe Majalisar Zartarwan Jiharsa, Ya Nemi a Yafe Masa

Gwamna Zulum Ya Rushe Majalisar Zartarwan Jiharsa, Ya Nemi a Yafe Masa

  • Gwamnan jihar Brono, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya sallami baki ɗaya mambobin majalisar zartarwa na jiha
  • Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kaɗan gabanin sake rantsar da Zulum karo na biyu a matsayin gwamnan Borno ranar 29 ga watan Mayu, 2023
  • A wata sanarwa da ofishin sakataren gwamnatin Borno ya fitar, gwamna ya yaba wa mutanen bisa gudummuwar da suka bayar

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya rushe majalisar zartaswan jiharsa kwanaki kalilan gabanin karewar zangonsa na farko.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan matakin da gwamna Zulum ya ɗauka zai fara aiki nan take a lokacin da mai girma gwamna ya amince.

Farfesa Babagana Zulum.
Gwamna Zulum Ya Rushe Majalisar Zartarwan Jiharsa, Ya Nemi a Yafe Masa Hoto: Babagana Zulum
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban Sakataren sashin shugabanci da harkokin bai ɗaya, Danjuma Ali, a madadin Sakataren gwamnatin Borno.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Tara Kwamishinoni da Hadimansa, Ya Tona Asirin Waɗanda Suka Ci Amanarsa

Sanarwan ta umarci mambobin, waɗanda suka ƙunshi kwamishinoni, SSA, SA da sauran hadimai, su miƙa harkokin ragamar jagorancin ma'aikatunsu ga manyan Sakatarori.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Zulum ya yaba tare da miƙa godiyarsa ga mambobin majalisar zartarwan bisa dumbin gudummuwan da suka baiwa gwamnatinsa a lokacin da suka shafe kan muƙamansu.

Haka nan kuma ya musu Addu'a tare da fatan Alheri a dukkan harkokin rayuwa da zasu fuskanta nan gaba bayan barin ofis.

Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan gabanin zangon farko na mulkin gwamna Babagana Umaru Zulum ya ƙare ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

A wannan rana ake sa ran zai sake karɓan rantsuwar kama aiki a matasayin gwamnan jihar Borno da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya zango na biyu.

Zulum na ɗaya daga cikin gwamnonin jam'iyyar APC a arewacin Najeriya da Allah ya sake baiwa damar samun nasara a babban zaben 2023.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Halarci Taron Zababɓen Gwamnan APC, Ya Yi Magana Mai Jan Hankali, Bayanai Sun Fito

Kotun Koli a Najeriya Ta Yanke Hukunci Kan Halascin Takarar Tinubu da Shettima a 2023

A wani rahoton na daban kuma kun ji cewa Kotun Koli ta yi watsi da karar da PDP ta nemi a soke tikitin Tinubu da Shettima.

PDP ta ɗaukaka kara zuwa Kotun koli bisa zargin cewa Shettima ya tsaya takara biyu a 2023 kuma ya saɓa wa dokar zaɓe 2022.

Amma da take yanke hukunci, Kotun ƙoli ta ce PDP ba ta da hurumin shigar da ƙara kan lamarin sabida ba mambar APC bace, bisa haka ta yi watsi da ƙarar baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel