Ya Kamata Tinubu Ya Dau Mataki Kan Emefiele da Wasu Jiga-Jigai, Smart

Ya Kamata Tinubu Ya Dau Mataki Kan Emefiele da Wasu Jiga-Jigai, Smart

  • Sanatan Kogi ta yamma, Smart Adeyemi, ya shawarci Tinubu ya ɗauki mataki kan duk mai hannu a kirkiro tsarin sauya fasalin naira
  • Ya ce akwai bukatar zababɓen shugaban ƙasa ya zaunar da gwamnan CBN da sauran masu hannu su masa bayanin komai
  • A cewarsa dama an kawo tsarin ne domin yaƙar burin Tinubu na zama shugaban kasa a zaben 2023

Kogi - Sanata Smart Adeyemi ya yi kira ga zababben shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya titsiye gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Bayan gwamnan CBN, Sanatan ya buƙaci Tinubu ya ɗauki matakai kan duk wanda ke da hannu wajen ƙuntata wa yan Najeriya ta hanyar kawo tsarin sauya fasalin takardun naira.

Emefiele.
Ya Kamata Tinubu Ya Dau Mataki Kan Emefiele da Wasu Jiga-Jigai, Smart Hoto: channelstv
Asali: UGC

Ɗan majalisar mai wakiltar Kogi ta yamma a majalisar dattawa ya faɗi haka ne sakamakon ƙaƙaba tsarin canjin kuɗi, wanda ya wahal da mutane duk da sukar tsarin.

Kara karanta wannan

Gwamna Arewa Ya Kori Kwamishinoni da Hadimansa Daga Aiki, Ya Ba Su Umarni Nan Take

A cikin shirin Politics Today na kafar watsa labaran Channels TV, Sanatan ya koka bisa tashe-tashen hankulan da suka faru sakamakon karancin takardun naira a hannun jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da aka tambaye shi wane mataki zai ɗauka kan tsarin canjin kuɗi idan da shi ne a matsayin Bola Tinubu, Sanata Adeyemi ya ce:

"Zan kira Emefiele da sauran kusoshin gwamnati masu hannu, su zo su mun bayani dalla-dalla kan abinda ya faru da kuma maƙasudin kawo tsarin canja takardun naira."
"Mutane sun mutu a wannan lokacin, wasu sun kamu da ciwon shanyewar jiki saboda ba su da ikon amfani da kuɗinsu. Saboda ni da kai mun tsira, ba zamu bi haƙƙin waɗanda suka mutu ba?"
"Wasu tilasta musu a ka yi suka mutu saboda wahalhalun da aka shiga a wancan lokacin, tsarin ya yi ajalin mutanen da ba su ji ba, basu gani ba."

Kara karanta wannan

To Fa: Gwamnan Arewa Na PDP Ya Magantu Kan Yuwuwar Ya Koma Jam'iyyar APC

Meyasa CBN ya kawo tsarin sauya fasalin naira?

A cewarsa, ɓangaren shari'a ne ya ceto ƙasar nan daga shiga wani yanayi, inda ya ƙara da ikirarin cewa an kirkiri tsarin canja naira ne domin yaƙar takarar Tinubu.

A rahoton Dailypost, Sanatan ya ci gaba da cewa:

"Bai kamata Tinubu ya manta da wannan ba, sun kaƙaba tsarin nan domin kar APC ta ci zaɓe amma bayan hukuncin Kotun koli zuwa yanzu, komai ya gushe."

"Na Shirya Zuwan EFCC," Gwamna Samuel Ortom

A wani labarin na daban Gwamna Ortom ya bayyana cewa ya shirya amsa gayyatar EFCC a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Idan baku manta ba EFCC ta ce akwai gwamnonin da ta sanya wa ido, tana jira su sauka mulki ta dirar musu.

Gwamna Ortom na jam'iyyar PDP ya ce baya tsoron kowa, kuma ba zai je ko ina ba da nufin tsere wa EFCC ba.

Kara karanta wannan

"Najeriya Zata Ƙara Bunkasa," Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Tinubu Wasu Kalamai Masu Kyau

Asali: Legit.ng

Online view pixel