Jerin Manyan ’Yan Siyasa a Najeriya da Suka Mallaki Jami’o’i Masu Zaman Kansu

Jerin Manyan ’Yan Siyasa a Najeriya da Suka Mallaki Jami’o’i Masu Zaman Kansu

  • Jami’o’in gwamnati a Najeriya suna fama da matsaloli da suka hada da yajin aikin malamai da lalacewar gine-gine
  • Sauran matsalolin sun hada da lalacewar dakunan gwaje-gwaje da rashin isassun kayan aikin da za su taimaka wa dalibai
  • Wadannan matsalolin suna shafar karatun dalibai musamman wurin shafe shekaru da dama kafin su kammala karatu

Abuja - Gwamnatoci da dama sun gagara kawo karshen matsalar jami'o'in gwamnati yayin da jami’o’i masu zaman kansu kullum ke kara yawa a kasar don rage ko kuma kawo karshen matsalolin.

Legit ta tattaro cewa Najeriya tana da akalla jami’o’i masu zaman kansu fiye da 100 da gwamnati ta amince dasu kamar yadda Hukumar Jami’o’in Najeriya (NUC) ta tabbatar.

Atiku, Obasanjo da sauran 'yan siyasa da suka mallaki jami'o'i
Yan Siyasa a Najeriya da Suka Mallaki Jami’o’i Masu Zaman Kansu. Hoto: @ronuspirit, @PeterObi.
Asali: Twitter

Abin burgewa, jami'o'i masu zaman kansu sun samu karbuwa sosai ganin yadda suke kawo ci gaba a harkokin ilimi da kuma samar da kudaden shiga ga gwamnati da kuma su kansu, ‘yan siyasa da dama sun shiga harkar gina jami’o’i masu zaman kansu saboda wadannan dalilai.

Kara karanta wannan

Gwamna El-Rufai Ya Zargi Tsoffin Gwamnonin Jihar da Satar Kudaden Al’umma Don Gina Gidaje a Dubai

Ga jerin manya-manyan ‘yan siyasa a Najeriya da suka mallaki jami’o’i masu zaman kansu a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’ar Fasaha ta Bells (Olusegun Obasanjo)

Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo shi ya mallaki jami’ar fasaha ta Bells da ke Ota cikin jihar Ogun.

An kafa jami’ar a shekara ta 2005.

Jami’ar Amurka ta Najeriya, AUN (Atiku Abubakar)

Atiku Abubakar wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne a Najeriya shi ya mallaki jami’ar Amurka ta Najeriya wadda da aka fi sani da ABTI kafin a sauya mata suna zuwa AUN.

Jami’ar da ke Yola babban birnin jihar Adamawa an kafa ta ne a shekarar 2003.

Jami’ar Baze (Yusuf Datti Baba-Ahmed)

Dakta Yusuf Datti Baba-Ahmed, mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour shi ne ya assasa wannan jami’a wadda aka kafa ta a shekarar 2011.

Jami'ar mai zaman kanta tana nan a Jabi da ke cikin Abuja babban birnin kasar.

Kara karanta wannan

Ana Binciken ‘Dan Takaran Gwamnan da Ya Kashe N2bn Ya Saye Kuri’u a Zaben 2023

Jami’ar Eastern Palm (Rochas Okorocha)

Tsohon gwamnan jihar Imo kuma Sanata da ke wakiltar jihar a majalisar dattawa shi ya kafa wannan jami’a a shekarar 2017.

Sai dai, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma yana zargin cewa jami’ar ba mallakin tsohon gwamnan bane bisa zargin badakalar cin hanci da rashawa, dalilin haka ne ma ya sa gwamnatin jihar ta sauya wa jami’ar suna zuwa jami’ar Kingsley Ozumba Mbadiwe.

Jerin Sunayen Attajiran Da ke Siyasa a Zaɓen 2023 na Najeriya

A wani labarin, a zaben shekarar 2023, daruruwan 'yan siyasa za su fafata a zaben da ke karatowa a kujeru daban-daban.

Mafi yawa daga cikinsu attajiran 'yan kasuwa ne wadanda suka shiga harkar siyasa don tsayawa ko marawa wasu daga cikin 'yan siyasa baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel