Gwamna El-Rufai Ya Zargi Tsoffin Gwamnonin Jihar da Satar Kudaden Al’umma Don Gina Gidaje a Dubai

Gwamna El-Rufai Ya Zargi Tsoffin Gwamnonin Jihar da Satar Kudaden Al’umma Don Gina Gidaje a Dubai

  • Gwamna Nasiru El-Rufai ya kalubalanci gwamnatocin baya a jihar Kaduna da satar kudin jihar
  • Gwamnan ya ce dukkansu babu wanda bai saci kudin al’umma ya gina gidaje masu alfarma ba
  • El-Rufai ya yabawa gwamnatinsu duba da irin ayyukan ci gaba da suka kawo a jihar masu inganci

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya zargi gwamnatocin baya a jihar da satar makudan kudade a lalitar gwamnati don gina gidaje a Dubai.

El-Rufai ya bayyana haka ne a yayin hirarsa ta karshe a matsayinsa na gwamnan jihar Kaduna.

Nasir El-Rufai na Kaduna
El-Rufai Ya Zargi Tsoffin Gwamnonin Jihar da Satar Kudaden Al’umma. Hoto: Daily Trust.
Asali: Facebook

Gwamnan ya kalubalance su da su rantse da Kur’ani mai tsarki idan har ba su saci kudin al’umma ba a lokacin mulkinsu, cewar Daily Trust.

Gwamnan ya ce tsoffin gwamnoni a jihar sun saci kudin al'umma

Kara karanta wannan

Na Rantse Ban Saci Ko Kobo Ba Daga Lalitar Jihar Kaduna, In Ji Gwamna El-Rufai

A cewarsa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“A ina suka samu kudade suka gina wadannan manyan gidajen alfarma? Wani irin kasuwanci suke yi? Mun sani.”

Tribune ta tattaro cewa gwamnan ya yabi kansa akan kawo abubuwan ci gaba da ya yi a jihar, inda ya kara da cewa ya ninka ayyukan da magabatansa suka yi wa ‘yan jihar a lokacinsa.

Ya kara da cewa:

“Ina murna akan abubuwan da nake gani. Ayyukan da muka faro da kuma ingancinsu, tabbas za a shafe shekaru da dama ana morarsu.
“Ba kalan hanyoyi da suka yi a baya ba, irin wadanda bayan damina biyu, duk hanyoyin za su lalace, ayyukan da muke yi masu inganci ne."

El-Rufai ya ce gwamnatinsu ta yi abin kirki

A cewarsa:

“Ina jin dadin abin da nake gani, duk da haka akwai sauran aiki saboda muna son mutanen Kaduna su ga babu wata hanya a lalace, “Muna son shimfidaddiyar kwalta a kowane yanki a jihar da wuta mai amfani da hasken rana, har da yankunan Kafanchan da Zaria da sauran kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Ba A Je Ko Ina Ba, An Fara Zargin Gwamnan APC Da Yakar Gwamna Mai Jiran Gado

“Duk wasu kudade da muka samu ko daga kudaden shiga ko daga birnin Abuja ko kuma bashi da muka karbo, na rantse da Allah mun yi amfani da su yadda ya dace, ba mu dauki ko kwabo daya ba, kuma ba mu sayi gidaje ba, ba ma bukatan wannan.”

Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Tayar Masa Da Hankali Lokacin Zabe

A wani labarin, gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana yadda aka yi amfani da kudi wajen siyan kuri'u a zaben da ya gabata.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Lahadi 21 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel