Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn Domin Siyo Motocin Alfarma

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn Domin Siyo Motocin Alfarma

  • Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba ya bayyana gaskiya kan rahoton cewa ya amince da fitar N2bn domin siyawa kansa da mataimakinsa motocin alfarma
  • Gwamnan wanda zai bar kujerar mulki ranar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, ya ce babu ƙanshin gaskiya a rahotannin
  • Ya bayyana cewa ƙage ne kawai na ƴan kanzagin soshiyal midiya masu son ganin sun tada fitina

Taraba, Jalingo - Gwamna Darius Ishaku, ya yi martani kan zargin cewa ya amince da fitar da N2bn a asusun jihar domin siyowa kansa, mataimakinsa da matansu, motocin kece raini duk da cewa wa'adin mulkin su ya kusa ƙarewa.

Gwamnan wanda ɗan jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ne, ya yi martanin ne ta hannun mai bashi shawara na musamman, Bala Dan-Abu, a ranar Lahadi, 14 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta 10: Abbas Da Kalu Sun Ziyarci Fitaccen Gwamnan APC, Sun Nemi Wata Muhimmiyar Alfarma 1

Gwamnan jihar Taraba ya musanta siyo motocin N2bn
Darius Ishaku ya musanta batun siyo motocin N2bn Hoto: Governor Darius Dickson Ishaku, Jautos and Top gear
Asali: Facebook

A cewar rahoton Punch, Dan-Abu ya bayyana cewa rahotan ƙanzon kurege ne waɗanda wasu ƴan kanzagi suka shirya shi.

A kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ba ma son kafafen watsa labarai su ɗauke shi da muhimmanci. Babu komai a cikinsa face ƙarya. Labarin ƙagen kawai wasu masu rubutu a soshiyal midiya ne."

Jam'iyyun adawa sun caccaki gwamnan kan fitar da kuɗin

Da ya ke magana dangane da lamarin, shugaban jam'iyyar Action Alliance Party (AA), Moses Kugba, ya bayyana cewa fitar da kuɗin ya saɓa da halin da jihar ta tsinci kanta a ciki, inda ake bin ta bashin kuɗaɗen fansho da gratuti na ma'aikata.

A kalamansa:

"Gwamna yana da hurumin samun motocin ofis, amma yanzu ba lokacin siyan su ba ne. Gwamnan yana da ayyukan da bai kammala ba, mu na tsammanin cewa zai ƙarasa waɗannan ayyukan, ba wai ya cire waɗannan maƙudan kuɗaɗen ba domin siyo motoci."

Kara karanta wannan

Ta Fasu An Ji: An Fallasa Abinda Tinubu da Gwamna Wike Su Ke Kulla Wa Atiku Abubakar a Kotu

Gabanin Miƙa Mulki, Gwamnan PDP Ya Kaddamar da Aikin da Ba'a Gama Ba

A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Taraba ya ƙaddamar da aikin da ba a kammala ba.

Gwamna Darius Dickson Ishaku, ya ƙaddamar da rukunin gidajen da ya ke ginawa a birnin Jalingo, duk kuwa da cewa ba a kammala aikin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel