CAN: Kungiyar Kiristoci Ta Sanar da Bola Tinubu Abubuwan da Ta ke Bukata a Mulkinsa

CAN: Kungiyar Kiristoci Ta Sanar da Bola Tinubu Abubuwan da Ta ke Bukata a Mulkinsa

  • Shugaban kungiyar CAN ya na so Bola Ahmed Tinubu ya yi adalci idan ya zama shugaban Najeriya
  • Daniel Okoh ya ba gwamnati mai zuwa shawara ta ba kowa hakkinsa ba tare da nuna bambanci ba
  • Idan zababben shugaban kasar ya shiga ofis, Bishof Daniel Okoh ya na so ya wanzar da zaman lafiya

Abuja - Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya na kasa watau CAN, ta yi kira da babban murya ga Bola Ahmed Tinubu wanda yake shirin karbar mulki.

Rahoto ya zo daga Sun cewa kungiyar CAN ta bukaci zababben shugaban kasar ya tabbata ya bi dokar daidaito a rabon mukamai idan ya dare karaga.

Wannan kungiya ta kiristoci ta ce akwai bukatar Gwamnati mai jiran-gado ta rika amfani da malaman addini wajen kawo zaman lafiya ga al’umma.

Kara karanta wannan

Kwanaki 13 Kafin Ya Bar Aso Villa, Buhari Ya Fadi Kokari 3 da Ya Yi Cikin Shekaru 8

Bola Tinubu
Bola Tinubu a coci Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Shugaban CAN na kasa, Bishof Daniel Okoh ya yi wannan kira a makon nan yayin da yake jawabi a wajen taron da wata gidauniyar ta shirya a garin Abuja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daniel Okoh ya na so kowane mutumin Najeriya ya amfana da romon tattalin arziki da zamantakewar rayuwa a ko ina yake rayuwa a jihohin kasar nan.

This Day ta ce shugaban na CAN ya na so gwamnatin Bola Tinubu ta yaki sabanin kabilanci da addini.

A jawabinsa, Okoh ya nuna Najeriya ta na da dinbin malamai da shugabannin addini da suke neman zaman lafiya, ya ce ya kamata ayi amfani da su.

Jawabin Shugaban CAN

"A girmama dokar daidaito wajen rabon mukamai da albarkatu kuma a ba ‘yan kasa damar yin imani ko ibada ba tare da an tursasa su ba.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Ba Tinubu Shawarwarin Abubuwan da Zai Yi Idan Ya Hau Kan Mulki

Duniya ta daina yayin dauke mutane, auren dole ko tursasa mutane wajen karbar addinin da ba su so, bai dace a kyale a rika yin su a nan ba.
A shawo kan lamarin shaidar zama ‘dan wuri da kuma ba ‘Yan Najeriya cikakken hakkin zama a wuri zai taimaka wajen kawo cigaba."

- Daniel Okoh

Makasudin wannan taro

Jaridar Guardian ta ce shugaban na kungiyar CAN ya na zargin ana fitar da jama’a daga addininsu da karfi da yaji musamman a jihohin Arewacin Najeriya

Shugaban gidauniyar da ta shirya zaman nan, Gideon Para-Mallam, ya ce sun kira taron ne a dalilin barnar da Boko Haram da wasu miyagu su ke aikatawa.

Emeka Ngige zai koma CLE

A makon nan ne labari ya zo cewa Cif Emeka Ngige (SAN) ya yi dace Shugaba Muhammadu Buhari ya tsawaita wa’adin mukaminsa a majalisar CLE.

An kara wa’adin shugaban na CLE da sauran ‘Yan majalisarsa da suka kunshi Kwamishinonin shari’a daga duka Jihohi 36 da kuma wakilai daga NBA.

Asali: Legit.ng

Online view pixel