CLE: Wa’adi Ya Zo Karshe, Buhari Ya Sake ba Ngige Matsayi a Gwamnatin Tarayya

CLE: Wa’adi Ya Zo Karshe, Buhari Ya Sake ba Ngige Matsayi a Gwamnatin Tarayya

  • Emeka Ngige (SAN) zai sake shafe karin shekaru hudu ya na jagorantar majalisar shari’a ta CLE a Najeriya
  • Shugaba Muhammadu Buhari ya amince shugaban na CLE ya zarce a kan kujerar da yake kai zuwa 2027
  • Cif Ngige da 'yan majalisarsa za su cigaba da kula da majalisar da ke da nauyin kula da harkar ilmin shari’a

Abuja - A lokacin da mulkinsa ya zo karshe, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake nada Emeka Ngige (SAN) a matsayin shugaban CLE.

This Day ta ce Cif Emeka Ngige (SAN) zai kuma yin shekaru hudu a ofis. Majalisar CLE ce ta ke da hurumin kula da hakar ilmin shari’a a Najeriya.

Baya ga Kwamishinonin shari’a na Jihohi 36 da ke cikin majalisar, CLE ta na kunshe da wakilai 17 daga kungiyar Lauyoyi na Najeriya watau NBA.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu: Kashim Shettima Ta Faɗi Kuskuren da Shugaba Buhari Ya Tafka a Mulkinsa Kamar Na Jonathan

Shugaban Najeriya
Shugaban Najeriya a Aso Rock Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Wakilan NBA sun hada shugaban kungiyar na kasa, Yakubu Maikyau SAN, babban marubucin nan, Sebastine Hon SAN da Olufunmilayo Roberts.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton ya ce Paul Harris Adakole Ogbole SAN yana cikin wakilan lauyoyi da ake da su a majalisar.

Ngige ya sanar da nadin da yake jawabi wajen taron da CLE ta shirya a karshen makon jiya a hedikwatar makarantar koyon aikin shari’a a Bwarai.

An shirya liyafa ta musamman a garin Abuja domin yin ban-kwana da wadanda suka jagoranci ragamar kungiyar tsakanin shekarar 2019 da 2023.

Guardian ta ce nadin ya na zuwa ne bayan an amince Isa Chiroma SAN ya sake yin shekaru hudu a matsayin shugaban makarantar koyon aikin shari’a.

Majalisar CLE da hadin-gwiwar makarantar da Farfesa Isa Chiroma SAN yake jagoranta ne su ke shirya jarabbawar da ake yi Lauyoyi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanatoci 3 da Hukumar EFCC ke Nema Sun Zama ‘Yan Gaba a Takarar Majalisar Dattawa

Har ila yau, majalisar ce ke da hakkin ba jami’o’in da ke kasar nan damar koyar da ilmin shari’a. Wa’adin Ngige zai cika a 2027 bayan shekaru hudu.

Mun kafa tubali - Buhari

An rahoto Muhammadu Buhari yana cewa sun samu cigaba daga lokacin da su ka shiga ofis a 2015, amma ya ce akwai gargada a hanya saboda rashin kudi.

Mai girma Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta maida hankali a bangarorin abubuwan more rayuwa, harkar gona da karfin soja saboda inganta tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel