Jam'iyyar PDP Ta Sanar Da Yin Azumi Na Kwana 7 Don Samun Nasara a Kotu

Jam'iyyar PDP Ta Sanar Da Yin Azumi Na Kwana 7 Don Samun Nasara a Kotu

  • Jam’iyyar adawa ta PDP ta sanarda yin azumi da addu’o’i na kwana bakwai don samun nasara a kotu
  • Addu’o’in za a gudanar da su ne a majami’ar dake sakatariar jam’iyyar a Wadata Plaza a ranar Laraba
  • Shugaban Kiristocin jam’iyyar PDP na kamfen din shuagaban kasa, Boni Haruna ne ya sanar da hakan

Abuja - Majami’ar jam’iyyar PDP ta kasa ta sanarda yin azumin mako guda da addu’o’i don samun nasarar tsohon mataimakin shugaban kasa a kotun sauraron kararrakin zabe.

Jaridar Punch ta tattaro cewa za a fara addu’o’in ne daga ranar Alhamis 18 ga watan Mayu zuwa ranar Laraba 24 ga watan Mayu.

Atiku Abubakar/Jam'iyyar PDP/Zaben Shugaban Kasa/Siyasa
Jam'iyyar PDP za ta yi addu'a da azumi na kwana bakwai don neman nasarar Atiku a kotu. Hoto: TVC News
Asali: Facebook

Addu’o’in za a gudanar da su ne a majami’ar jam’iyyar dake sakatariyar jam’iyyar a Wadata Plaza da ke Abuja da misalin karfe 12 na rana a kullum.

Kara karanta wannan

Atiku Bai Cire Rai Ba, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Ya Faɗi Abu 1 Rak da Zai Baiwa PDP Nasara a Kotu

Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP sun shigar da kara a kotun suararen korafe-korafen zabe akan zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta INEC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An daga sauraron kararrakin zaben zuwa 18 ga watan Mayu don ci gaba da sauraren karar da jam’iyyar PDP ta shigar kan jam’iyyar APC mai mulki da zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

Boni Haruna ya ba da sanarwa

Shugaban Kiristocin jam’iyyar PDP na kwamitin kamfen na shugaban kasa, Boni Haruna ne ya sanar da fara wannan azumi da addu’o’in kwana bakwai don samun nasara a kotu.

“Musabbabin yin wannan addu’o’i da azumi shi ne don bijirewa cankan Bola Tinubu da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta yi da kuma ceto da dawo da jam’iyyar PDP.
“Za a dauki ayoyi daga Romawa sura 8 aya 33, da Psalms sura 84 aya 10 zuwa 11, sai kuma Proverbs sura 24 aya 25 zuwa 26, da sura 9 aya 7 zuwa 8", in ji shi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Yi Hasahen Wanda Zai Samu Nasara a Kotu Tsakanin Tinubu da Atiku, Ya Faɗi Hujja

"Atiku Shi Kadai Ya Kashe PDP Ya Kuma Binneta Tun 1999": Fani-Kayode Ya Zolayi Atiku

A wani labarin, Femi Fani Kayode ya yi ba'a ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kan yadda ya kashe PDP har ya binneta yadda ba zata sake tashi ba.

Tsohon ministan ya kara da cewa 'yan Najeriya dole su godewa Atiku saboda yadda ya nakasa jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel