Gwamna Tambuwal Ya Yi Hasahen Hukuncin da Kotu Zabe Zata Yanke Kan Nasarar Tinubu

Gwamna Tambuwal Ya Yi Hasahen Hukuncin da Kotu Zabe Zata Yanke Kan Nasarar Tinubu

  • Jiga-jigan babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa sun fara sa ran kotun sauraron karar zaben shugaban kasa zata ba su nasara
  • Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sakkwato yace yana da yaƙinin Kotu zata maida wa PDP hakkinta kuma Atiku zai samu adalci
  • Jagororin jam'iyyar PDP a wurin taron da suka gudanar a Abuja, sun jaddada cewa shari'a ce kaɗai gatan mara galihu a Najeriya

Abuja -Shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP kuma gwamnan Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya yi hasahen hukuncin da Kotun zabe zata yanke kan karar zaben shugaban kasa a Najeriya.

Tambuwal ya ce yana da kwarin guiwa Kotu zata maida wa ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, haƙƙinsa na zama shugaban Najeriya, rahoton This Day.

Taron APC a Abuja.
Gwamna Tambuwal Ya Yi Hasahen Hukuncin da Kotu Zabe Zata Yanke Kan Nasarar Tinubu Hoto: Abdul Rasheeth
Asali: Twitter

PDP ta fara jin ƙanshin nasara a Kotun zaɓe

Gwamnan ya yi wannan kalamai a wurin taron liyafar da ƙungiyar gwamnoni ta shiryawa gwamnoni masu jiran gado da waɗanda wa'adinsu ke dab da ƙarewa, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Abubakar da Wasu Fitattun Gwamnoni Sun Dira Wurin Liyafa, Bayanai Sun Fito

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka nan a wurin wannan liyafa, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku, ya tabbatarwa mahalarta taron cewa PDP zata kwato nasararta, saboda jam'iyar ba ta sha kashi a zaben 25 ga watan Fabrairu ba.

A kalamansa, gwamna Aminu Tambuwal ya ce:

"Muna da kwarin guiwar cewa a karshen karshe, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, zai dawo da haƙƙinsa kamar yadda kundin mulkin Najeriya ya tanada."
"Ga dukkan alamu da abunda muke gani a zahiri, muna da yaƙinin nasara zata dawo, muna kallonsa a matsayin shugaban ƙasa mai jiran gado."

Bayan INEC ta sanar da Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya ci zaben shugaban kasa, Atiku da takwaransa na LP, Peter Obi, suka nufi Kotun zabe.

Manyan yan takarar biyu da suka zo na biyu da na uku a zaben, sun lashi takobin kalubalantar nasarar Tinubu, domin a cewarsu an tafka kura-kurai.

Kara karanta wannan

Atiku da Gwamna Wike Zasu Haɗu a Karon Farko Bayan Babban Zaben 2023, Bayanai Sun Fito

Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet

A wani labarin kuma Kotun Koli a Najeriya Ta Yanke Hukunci Kan Rigimar Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet

Yayin yanke hukunci kan ƙarar zaben gwamnan Osun ranar Talata, Kotun ta ce ba dole bane sai INEC ta ɗora sakamakon zabe a shafin yanar gizo-gizo.

A cewar Alkalin Kotun babu dokar da ta tilastawa hukumar zabe (INEC) ta tura sakamako kai tsaye daga rumfunan zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel