Rundunar Soji Ya Magantu Kan Masu Shirin Hana Bikin Rantsar da Tinubu

Rundunar Soji Ya Magantu Kan Masu Shirin Hana Bikin Rantsar da Tinubu

  • Hukumar sojin Najeriya ta ce bikin rantsar da zababben shugaban kasa ranar 29 ga watan Mayu, 2023 zai zo kuma ya wuce, ba abinda zai faru
  • Hukumar ta ce duk masu tunanin kawo cikas a bikin rantsarwan su sauya tunani domin Sojoji ba zasu bar ƙofa ɗaya ba
  • Rundunar sojin ta kuma gargaɗi yan siyasa da masu ruwa da tsaki cewa dakarunta zasu zauna a shirin ko ta kwana

Abuja - Hukumar sojin Najeriya ta aike da sakon gargaɗi ga yan siyasa da wasu fitattun 'yan Najeriya, waɗanda ta ce suna da hannu a yunkurin ta da yamutsi ranar miƙa mulki, 29 ga watan Mayu, 2023.

Hukumar sojin ta gargaɗi waɗan nan mutane da babbar murya cewa su gaggauta ɓinne shirinsu a cikin zuciyarsu, domin idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira.

Kara karanta wannan

Yadda Kasar Masar Ta Umarci Ɗaliban Najeriya Sama da 500 Su Koma Sudan Kan Halayyar Mutum 2

Tinubu da Farouk Yahaya.
Rundunar Soji Ya Magantu Kan Masu Shirin Hana Bikin Rantsar da Tinubu Hoto: Nigeria Army
Asali: Twitter

Ta ce dakarun soji sun shirya dakile duk wani motsi da ba'a buƙata a kasar nan, la'alla gabani, ranar ko bayan rantsar da zababben shugaban ƙasa a karshen watan nan, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Me rundunar soji ta faɗa game da bikin miƙa wa Tinubu mulki?

Manjo Janar Musa Ɗanmadami, daraktan sashin midiya na hukumar tsaro a Najeriya, ne ya yi wannan gargaɗi ga yan siyasa yayin zantawa da yan jarida bayan kammala taron mako bibbiyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba mako biyu da suka gabata, Hedkwatar tsaro ta ƙasa ta kara jaddada shirinta na murkushe duk wanda ta kama da hannu a kokarin ruguza bikin rantsarwa.

Da yake jawabi ranar Alhamis 4 ga watan Mayu, Danmadami ya ce babu wani da zai gamsar da rundunar soji wanda zai hana rantsar da shugaban ƙasa mai jiran gado.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Gargaɗi 'Yan Siyasar Da Ke Shirin Kawo Cikas Ga Rantsar Da Shugaban Ƙasa

Sojoji sun shirya tsaf

Ya ce rundunar yan sanda ce kan gaba wajen kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya amma sauran hukumomin tsaro zasu zauna cikin shiri don dakile duk wani motsi mai alamar tambaya.

A cewar daraktan, Dakarun soji zasu magance duk wani kalubalen tsaro da ka iya tasowa a wannan rana, inda ya ƙara da cewa zaɓe ya wuce kuma an bayyana wanda ya samu nasara.

A ruwayar This Day, wani sashin jawabinsa ya ce:

"Bamu ga wani dalilin da zai sa a samu matsala lokacin bikin ba. Rantsarwa zata zo ta wuce, kuma babu abinda zai faru."

Na Yi Kokarin Jawo Hankalin Tinubu Ya Dawo PDP a 2018, Gwamna Wike

A wani labarin kuma Gwamna Wike ya bayyana yadda ya yi koƙarin jawo hankalin Bola Tinubu ya bar APC zuwa PDP.

Gwamna Ribas ya ce har gidan Tinubu ya je suka gana don ya baro APC su haɗe a jam'iyyar PDP amma hakan ba ta samu ba.

Kara karanta wannan

"Ba Ka Bi Na Bashin Komai": Wasu Muhimman Abubuwa 5 Da Tinubu Ya Fada Yayin Da Wike Ya Gayyace Shi

Wike, mamban jam'iyyar PDP, wanda ke ɗasawa da zababben shugaban kasa, ya faɗi amsoshin da Tinubu ya ba shi a shekarar 2018.

Asali: Legit.ng

Online view pixel