Mahukunta a Kasar Masar Sun Maida Yan Najeriya 200 Zuwa Sudan

Mahukunta a Kasar Masar Sun Maida Yan Najeriya 200 Zuwa Sudan

  • Ɗaliban Najeriya biyu sun kawo babban cikas a yunkurun gwamnatin tarayya na dawo da su gida daga kasar Sudan
  • Bayanai sun nuna kasar Masar ta maida ɗaliban zuwa Sudan bayan kama biyu daga cikinsu ba su da Fasfo ko shaidar ETC
  • Tuni rukunin farko na yan Najeriya mazauna Sudan da suka tserewa yaƙin da ya barke suka iso Najeriya

Hukumomin ƙasar Masar sun umarci ɗaliban Najeriya sama da 500 su koma ƙasar Sudan biyo bayan gano biyu daga cikinsu ba su da Fasfo ko shaidar tafiya ta gaggawa (ETC)

A wani sakon muryar jami'in Najeriya, wanda ya shiga hannun wakilin jaridar Punch da safiyar Jumu'a 5 ga watan Mayu, duk ɗalibin da ba shi da Fasfo ko ETC, sun umarci ya koma inda ya fito.

Yan Najeriya a Sudan.
Mahukunta a Kasar Masar Sun Maida Yan Najeriya 200 Zuwa Sudan Hoto: Punchng
Asali: Facebook

Jami'in ya bayyana cewa ɗaliban biyu sun yi gajen hakuri ne amma da duk zasu samu takarkun da ake buƙata, kawai suka yi gaban kansu suka shiga tawagar ɗalibai.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Tare Hanya Cikin Dare, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

Ya ƙara da cewa a halin yanzun hukumomin ƙasar Masar sun fusata da rashin shaidar ɗaliban kuma sun umarci baki tawagar ƴan Najeriya sama da 500 su koma Sudan su nemo takardun izini.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin sakon sautin murya, an ji jami'in na cewa:

"Yaranmu sun ruguza kokarin gwamnatin tarayya na kwashe su a jirgi zuwa gida. Duk ɗalibin dake da Fasfo mun tura shi zuwa Masar, sannan wanda bai da shi mun ce ya jira zamu samar masa ETC."
"Amma saboda rashin haƙuri da gaggawa, biyu daga cikin ɗaliban suka faki ido suka shiga cikin tawaga kuma ba su da Fasfo ko ETC. Yanzu asirin su ya tonu a filin jirgin Aswan kuma hukumomin Masar sun fusata."
"Wannan matsala ta jawo dukkansu sai sun koma Sudan, sun haura mutum 500 amma duk sai sun koma Sudan sun karbi shaidar izinin fita daga ƙasar sannan kuma su karbi shaidar izinin shiga Masar. Sai sun ɓata awanni 10."

Kara karanta wannan

"Ba Ka Bi Na Bashin Komai": Wasu Muhimman Abubuwa 5 Da Tinubu Ya Fada Yayin Da Wike Ya Gayyace Shi

The Nation ta rahoto bayan daliban biyu, akwai wani mutum ɗaya da ya shiga tawagar ba tare da izini ba kuma har yanzun ba'a san inda ya shiga ba.

Gwamnatin Buhari Zata Tura Ƙarin Jiragen Sama Su Kwaso Yan Najeriya Daga Sudan

A wani labarin kuma Gwamnatin Najeriya ta ce zata tura ƙarin jirage domin kwaso ɗalibai daga ƙasar Sudan

Shugabar hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje ta ce ƙasar Masar ta gindaya shardin kwashe duk wanda ya shiga ƙasarta kuma ya yi tsauri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel