Na Yi Kokarin Jawo Hankalin Tinubu Ya Dawo PDP a 2018, Gwamna Wike

Na Yi Kokarin Jawo Hankalin Tinubu Ya Dawo PDP a 2018, Gwamna Wike

  • Gwamna Nyesom Wike na Ribas ya bayyana yadda ya yi yunkurin jan hankalin Tinubu ya sauya sheƙa daga APC
  • Wike, mamban jam'iyyar PDP ya ce ya yi bakin kokarinsa domin Tinubu ya dawo su haɗa kai a babban zaɓen 2019
  • Zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya kai ziyarar kwana biyu jihar Rubas, inda ya kaddamar da ayyukan Wike

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya tona yadda ya yi yunkurin jawo hankalin zababben shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya bar jam'iyyar APC zuwa PDP a 2018, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Ya ce ya gana da shugaban ƙasa mai jiran gado a shekarar 2018 a gidansa Bourdillon da ke jihar Legas da misalin karfe 2:00 na dare a yunkurin jawo hankalinsa ya koma PDP.

Bola Tinubu da Wike
Na Yi Kokarin Jawo Hankalin Tinubu Ya Dawo PDP a 2018, Gwamna Wike Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Wike ya faɗi wannan labarin ranar Laraba da daddare a gidan gwamnatinsa da ke Patakwal a wurin liyafar da aka shirya domin girmama zababben shugaban kasa, Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

"Ba Ka Bi Na Bashin Komai": Wasu Muhimman Abubuwa 5 Da Tinubu Ya Fada Yayin Da Wike Ya Gayyace Shi

Gwamnan ya ce nan take Tinubu ya yi fatali da tayin da ya masa bayan ya jero masa sunayen yan takarar shugaban kasa da ka iya lashe tikitin PDP a zaben 2019.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabinsa, gwamna Wike ya ce:

"A karon farko na gana da shi a 2018 da misalin karfe 2:00 na dare a gidansa Bourdillon. Jam'iyya ta tura ni na masa magana ko zai dawo mu haɗu."
"Yayin da na je wurinsa na faɗa masa yallabai na samu labarin ka rasa matsuguni a cikin APC, me zai sa ba zaka dawo cikinmu, mu haɗu mu marawa ɗaya daga cikin yan takara baya ya lashe zaben 2019 ba?"
"(Da Tinubu ya tashi bani amsa) Ya tambaye ni su waye ƴan takararku, na lissafo masa su. Ya faɗa mun idan waɗannan ne 'yan takarar mu, gara ya goyi bayan Buhari sau 200. Haka ya faɗa mun kuma na girmama shi.'

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran da Ake Zargi da Yi wa APC Aiki a 2023 Ya Fito Fili Yana Goyon Bayan Tinubu

PDP Ta Zabi Sabon Shugaban Jam'iyya a Jihar Osun

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta sanar da sabon shugaban jam'iyya a jihar Osun tare da Sakatarensa

A ranar Laraba 3 ga watan Mayu, 2023, PDP ta gudanar da gangamin taron zaben shugabanninta na jihar Osun, Deleget suka kaɗa kuri'a.

Bayan kammala kidaya kuri'u, kwamitin shirya zaɓen ya sanar da waɗanda Allah ya baiwa nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel