Labari Mai Zafi: Dino Melaye Ya Samu Takarar Gwamnan Jihar Kogi a Jam’iyyar PDP

Labari Mai Zafi: Dino Melaye Ya Samu Takarar Gwamnan Jihar Kogi a Jam’iyyar PDP

  • Dino Melaye shi ne ‘dan takaran jam’iyyar PDP a zaben sabon Gwamna da za a shirya a Kogi
  • Tsohon Sanatan zai kara da ‘Dan takaran APC wanda yake son zama magajin Yahaya Bello
  • Wannan karo jam’iyyar hamayya ta PDP ta fito da ‘Dan takarar Gwamna a Yammacin Kogi

Kogi - A zaben tsaida gwani na shiga takarar sabon Gwamna a jihar Kogi da jam’iyyar PDP ta shirya, an samu wanda ya yi nasara.

Rahoton Daily Trust na yammacin Lahadi ya bayyana cewa Sanata Dino Melaye shi ne wanda zai rikewa jam’iyyar PDP tuta a zaben Kogi.

Melaye yana da kuri'u 313 a zaben da aka yi a dakin taro na Kafa’s Hall da ke Lokoja.

Ahmed Makarfi ya ce Ilona Kingsley ya samu kuri'u 124, Usman Kabiru 121. Abayomi Awoniyi, Wada Musa, Ojaja Enama da Femi Olarewaju ba su kai labari ba.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Malamin Makarantar Da Ya Lashe Zaben Gwamnan Kebbi

Akwai irinsu James Faleke wadanda suka rika cewa ya kamata wannan karo ‘dan takaran Gwamnan Kogi ya fito daga Yammacin jihar.

A baya, Melaye ya taba zama ‘dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Kabba da Ijumu da kuma Sanata na jihar Kogi ta yamma a APC.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An ba 'Yan Kogi ta yamma takara

Kafin yanzu, a zaben 2019, tsohon ‘dan majalisar ya nemi tsayawa takarar Gwamnan jihar Kogi, amma sai Musa Wada ya yi galaba a kan shi.

Zaben 2023 ya zo da wani salo domin a cikin manyan jam’iyyun kasar, ba a samu wanda ta tsaida ‘dan kabilar Igala da aka sani da mulki ba.

Dino Melaye
Sanata Dino Melaye Hoto: @_Dino Melaye
Asali: Twitter

A 'yan kwanakin nan aka ga jigon na PDP ya shiga Kabba da yankin Kogi ta tsakiya domin samun goyon bayan masu tsaida 'dan takarar Gwamna.

Kara karanta wannan

Zaben cike gurbi: Jerin 'yan takarar da suka yi nasara a zaben jiya Asabar

Yayin da jam’iyyar APC ta ba ‘dan kabilar Ebira tuta, da alama 'yan kabilar Igala za su yi shekaru akalla 12 a jere ba tare da sun yi gwamna ba.

Dino v Ododo

A zaben 11 ga watan Nuwamban 2023, Dino Melaye zai gwabza da Ahmad Usman-Ododo wanda jam’iyyar APC mai-ci ta ba tikiti a jiya.

Usman-Ododo ya yi nasara a kan ‘yan takara da-dama, daga ciki har da Sanata Smart Adeyemi wanda ya fito yanki daya da shi Dino Melaye.

Sauran ‘Yan takaran da aka gwabza da su a APC sun hada da Stephen Ocheni, Sanusi Ohiare, Abubakar Achimugu da kuma Salami Ozigi.

'Yan takara sun janye

A baya ne aka ji labari cewa Edward Onoja wanda ake yi wa kallon na hannun daman Yahaya Bello a APC, ya fasa neman tikitin 2023.

Mutum 8 su ka janye takararsu a Jam’iyyar APC, tun daga nan aka gane cewa za a tsaida Ahmed Usman-Ododo ne a matsayin 'dan takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel