Jerin Wadanda Suka Yi Nasara a Zaben Cike Gurbin da Aka Gudanar a Najeriya

Jerin Wadanda Suka Yi Nasara a Zaben Cike Gurbin da Aka Gudanar a Najeriya

Wadanda suka yi nasara a zaben ranar Asabar 15 ga watan Afrilu sun fara fitowa, hukumar zabe ta fara bayyana wadanda za su hau mulki.

Mun tattaro muku jerin wadanda suka yi nasara, kuma za mu ci gaba da kara adadin duk sadda muka samu rahoto kan nasarar wani.

Yadda zaben bana ya kasance
Yadda ake kada kuri'u a Najeriya | Hoto: dailytrust.com
Asali: Depositphotos

Kujerun sanata

Hon Diket Plang

INEC ta ayyana Hon. Diket Plang na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe kujerar sanatan Filato ta tsakiya a cikon zaben bana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na fitowa ne daga sanarwar da Dr Jima Lar ya yi a Pankshin, hedkwatar Filato ta tsakiya kenan.

Ya bayyana cewa, Hon. Plang ya samu kuri’u 131,129 a zaben da aka kammala.

Abokin hamayyarsa na PDP, Yohanna Gotom ya samu kuri’u 127,022, yayin da Garba Pwul na Labour Party ya samu kuri’u 36,510.

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 7 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Malamin Makarantar Da Ya Lashe Zaben Gwamnan Kebbi

Ibrahim Bomai

Bomai na APC a jihar Yobe ya yi nasarar lashe kujerar sanatan Yobe ta Kudu a zaben da aka kammala jiya Asabar.

Bomai ya samu kuri’u 69,596, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na PDP da ya samu kuri’u 68,885 a zaben na jiya.

Aminu Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto na PDP, Aminu Tambuwal ya yi nasara zaben sanatan da aka kammala a jihar a jiya Asabar.

Tambuwal ya samu kuri'u 100,860, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na APC, Sanata Danbaba Dambuwa mai kuri'u 95,884.

‘Yan majalisun tarayya

Barista MB Shehu

A jihar Kano, dan takarar NNPP, Barista MB Shehu ne ya lashe zabe a mazabar tarayya ta Fagge a zaben da aka kammala jiya.

Shehu ya lallasa abokin hamayyarsa da ke kan kujerar ta dan majalisa, Aminu Sulaiman Goro, wanda yake neman sake komawa a karo na uku a karkashin jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Kebbi

Alhassan Ado Doguwa

A jihar ta Kano har ila yau, dan takarar APC kuma dan majalisan da ke son komawa a karo na biyar ya sake lashe zabe a mazabar Doguwa/Tudun Wada.

Wannan na zuwa ne a cikon zaben da aka kammala jiya, inda a baya aka sanar da soke zaben wasu yankunan saboda barkwar rikici.

A INEC, Doguwa ya samu kuri’u 41,573, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na PDP, Yushau Salisu na NNPP da ya samu kuri’u 34,831 a zaben.

Kujerun gwamna

Aisha Binani

A bangaren kujerun gwamna, Aisha Binani ce ta zama mace ta farko da ta taba zama gwamna a Najeriya, kuma daga Arewacin Najeriya.

An sanar da zaben ne a yau Lahadi bayan da aka dauki lokaci ana kai ruwa rana kan sakamakon zaben jihar ta Adamawa.

Dr Nasiru Idris

A jihar Kebbi kuwa, dan takarar jam'iyyar APC ne ya yi nasarar lashe zabe, inda ya lallasa abokin hamayyarsa na PDP.

Dr Nasiru Idris ya samu kuri'i 409,225 a zabe, inda abokin hamayyarsa, Aminu Bande ya samu kuri'u 360,940.

Asali: Legit.ng

Online view pixel