Abin da Ya Sa Na Tika Ka da Kasa a Takarar Shugaban Najeriya – Bola Tinubu ga Peter Obi

Abin da Ya Sa Na Tika Ka da Kasa a Takarar Shugaban Najeriya – Bola Tinubu ga Peter Obi

  • Asiwaju Bola Tinubu ya sanar da Peter Obi shi ba kanwar lasa ba ne idan ana maganar siyasa
  • Zababben shugaban kasar ya ce ya doke Jam’iyyar LP takaran 2023 ne saboda kafuwar da ya yi
  • Lauyan da Tinubu ya dauka, Wole Olanipekun, SAN ya zargi Obi da yawan sauya-sheka a siyasar

Abuja - Asiwaju Bola Tinubu yana kalubalantar ‘Dan takarar jam’iyyar LP a zaben shugaban kasan 2023, Peter Obi a kotu, yana so a soke takararsa.

Vanguard ta ce Asiwaju Bola Tinubu ya shigar da martaninsa tare da Kashim Shettima a gaban kotun da ke sauraron korafin zaben shugaban kasa.

Da yake bayani game da dalilin da ya sa ya yi nasara a takarar da suka shiga, Tinubu ya ce dadewa ana yi da tarihin da ya bari suka jawo masa karbuwa.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Ambato Mutum 2 da Suka Hana Atiku Zama Shugaban Najeriya

Lauyan ‘dan takaran na jam’iyyar APC, Wole Olanipekun, SAN ya fadawa kotu yayin da aka san Tinubu da manufa, shi kuwa Obi ya saba sauya-sheka.

Baya ga tsalle-tsallen da yake yi tsakanin wannan jam’iyyar siyasa zuwa wata, Olanipekun SAN ya ce ‘dan takaran LP bai da kafuwar da zai ci zabe.

Tarihin Tinubu a siyasa

Lauyan yake cewa a lokacin da Tinubu ya yi takarar Sanata a Legas a zaben 1992, ya samu kuri’un da suka zarce na duka ‘yan takarar majalisa a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da ya je majalisa kuwa, babban Lauyan ya ce wanda ake karewa a kotun ya rike shugabancin kwamitin harkar banki, tattalin arziki, da kasafin kudi.

Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu da Kashim Shettima Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Domin nuna irin jajircewarsa, Olanipekun ya ce ‘dan siyasar yana cikin wadanda suka kafa kungiyar NADECO wanda ta matsawa sojoji mika mulki.

Bayan dawowa mulkin farar hula ne Lauyan ya tunawa kotun zaben cewa wanda ake karar ya zama Gwamna a Legas, ya yi abin da har yau ake alfahari.

Kara karanta wannan

Zababben Shugaban Kasa, Tinubu Ya Shiga Cikin Mutum 100 da Suka Fi Tasiri a Duniya

Allura za ta tono garma?

Rahoton ya ce Lauyar da APC ta dauko ya soki jam’iyyar LP da ta ke korafi a kan sakamakon zaben Taraba, Adamawa, Bauchi da Kaduna, inda PDP ta ci.

Har ila yau, an ji cewa Tinubu yana so ayi fatali da rokon LP, sannan ayi bincike a kan jihohin da tsohon Gwamnan na Anambra ya samu galaba a takarar bana.

Obi 'Dan jam'iyyar PDP ne

Labari ya zo cewa sababben shugaban Najeriyan ya dogara da sashe na 77 na dokar zabe, ya ce LP ba ta bi ka’ida wajen bada tikitin takarar shugabancin kasa ba.

Lauyan da ya tsayawa ‘dan takarar jam’iyya mai mulki ya ce ‘dan takaran LP bai da rajista a jam’iyyance, domin a lokacin da aka ba shi takara, shi ‘dan PDP ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel