Na Shiga Uku: Nasarar APC Ta Jefa Ni Cikin Hadari Inji Tsohuwar Mataimakiyar Gwamnar Legas

Na Shiga Uku: Nasarar APC Ta Jefa Ni Cikin Hadari Inji Tsohuwar Mataimakiyar Gwamnar Legas

  • Sinatu Aderoju Ojikutu ta kira taron manema labarai, ta fadawa Duniya ta na fuskantar barazana
  • Tsohuwar mataimakiyar Gwamnar ta ce zaman Bola Tinubu zababben shugaban kasa hadari ne a gare ta
  • ‘Yar siyasar za ta cika alkawarin da ta dauka na cewa muddin Tinubu ya ci zabe, ta tashi daga ‘Yar Najeriya

Lagos - Alhaja Sinatu Ojikutu wanda ita ce macen farko da aka zaba a matsayin Mataimakiyar Gwamna a Najeriya, ta ce ta na fuskantar barazana.

Rahoton Daily Trust ya zo cewa Sinatu Ojikutu ta na ikirarin zaman Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zababben shugaban Najeriya, ya jefa ta a cikin hadari.

Alhaja Sinatu Ojikutu wanda ta rike Mataimakiyar Gwamna a lokacin Sir Michael Otedola tsakanin 1992 da 1993 za ta tashi daga zama ‘Yar Najeriya.

Kara karanta wannan

Mace Ta Fito Takarar Shugabancin Majalisa, Ita Kadai Za Ta Gwabza da Maza Kusan 10

Kamar yadda tayi alkawari, ‘yar siyasar ta ce ta fara shirye-shiryen watsar da takardunta na zama ‘yar Najeriya, ganin Bola Tinubu zai dare mulki.

Rikici mai dogon tarihi

Da ta zanta da manema labarai a gidanta da ke birnin Ikoyi a jihar Legas, Sinatu Ojikutu ta ce tun shekaru fiye 20 da suka wuce ta samu sabani da Tinubu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarta, dalilin kuwa shi ne ba ta goyi bayan ya yi takarar Gwamnan Legas ba, tun bayan lokacin ake kokarin ganin an sasanta su, amma abin ya faskara.

TINUBU
Bola Tinubu cikin masoya Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Ojikutu ta shaidawa jaridar cewa har Olusegun Obasanjo ya nemi ya yi masu sulhu, lamarin ya gagara.

Ganin cewa ranar 29 ga watan Mayun 2023, Tinubu zai dare kujerar shugaban Najeriya, Ojikutu ta ce babu shakka rayuwarta tana cikin halin barazana.

Kara karanta wannan

Sai ka shiga Villa: Duk duniya ba mai iya hana rantsar da Tinubu, inji fitaccen gwamnan APC

Na fito kafin zabe na fada cewa idan Bola Tinubu ya lashe zaben, ni Sinatu Aderoju Ojikutu zan tashi daga zama ‘yar Najeriya, kuma ina da dalilai na.
Lokacin da ya yi nasara, mutane sun kira ni suka fada mani ya ci, ba zai yi mani wani mugun abu ba, amma na san mutumin nan na sama da shekaru 20.
Na san irin abin da ya yi mani. Na kira taron nan domin in nuna hadarin da nake ciki a wanan yanayi, an hana ni sakat saboda Tinubu yana yaka ta.

- Sinatu Aderoju Ojikutu

An zargi APC da magudi

A wani rahoto, an ji Lauyan jam'iyyar nan ta APP ya ce APC tayi magudi a Kano, Kaduna, Kebbi, Ribas, Oyo, Ogun. Ekiti, Kogi da Kwara a zaben shugaban kasa.

Yanzu jam’iyyun da suka yi karar Bola Tinubu a kan zargin magudin zabe a 2023 sun kara yawa zuwa biyar. APP ta na so a rusa nasarar APC, a ba jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Tinubu Na Shirin Dawowa Kasar a Gobe Litinin Yayin da Ake Fafatawa Wajen Neman Shugabancin Majalisa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel