Makarkashiyar Gwamnonin PDP Ta Jawo Rikicin Cikin Gidan Jam’iyya Zai Koma Sabo

Makarkashiyar Gwamnonin PDP Ta Jawo Rikicin Cikin Gidan Jam’iyya Zai Koma Sabo

  • ‘Yan kungiyar G5 sun dage ayi sabon zaben shugabannin jam’iyyar PDP na kasa kwanan nan
  • Gwamnonin su na so su kora Iyorchia Ayu da yaransa daga mukaman majalisar NWC a Jam’iyya
  • Akwai irinsu Gwamnan Bauchi wanda ake zargin za su yaki duk wani shiri na canza shugabanni

Abuja - Akwai sabani sosai a jam’iyyar hamayya ta PDP inda wasu daga cikin Gwamnonin nan da aka fi sani da ‘Yan G5 suka zo da sabon batu.

Gwamnonin na G5 su na kokarin ganin an yi wani kwarya-kwaryan taron zaben shugabanni, za a samu wannan labarin a jaridar nan ta The Nation.

An dauko aikin ne domin a birne Dr Iyorchia Ayu, a daina jin duriyarsa a majalisar NWC, masu wannan shiri su na neman canza shugabanni na kasa.

Wasu daga cikin masu goyon bayan shugaban jam’iyyar PDP da aka dakatar, sun ce ba za ta yiwu a kira wannan taro alhali kara ta na gaban kotu ba.

Kara karanta wannan

Lambar Ministoci 2 Ya Fito da ‘Yan Majalisa Ke Binciken Satar Gangunan Mai Miliyan 48

An samu rabuwar kai a PDP

Idan ‘Yan G5 sun samu yadda suke so, za a fatattaki masu rike da NWC da ba su tare da su ko kuwa wadanda daga baya su ka bi tsagin Atiku Abubakar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Sanata Samuel Anyanwu yana cikin wadanda za a sauke shi daga kujerar da yake kai na Sakataren jam’iyya.

Gwamnonin PDP
Gwamnonin G5 a Benuwai Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Samuel Anyanwu zai bar wannan mukami ne bayan samun tikitin takarar Gwamnan jihar Imo.

A canza 'Yan NWC kafin a bada mulki

Rahoton ya ce gwamnonin nan biyar sun huro wuta, su na so ayi wa majalisar gudanarwar jam’iyyar ta PDP garambawul kafin 29 ga Mayun 2023.

Duka Gwamnonin G5 illa Mai girma Seyi Makinde za su bar ofis ne a watan Mayu.

Ana kishin-kishin yankin Ayu na Arewa maso tsakiya zai cigaba da rike shugabanci, ana tunanin harin shi ne a kai takara zuwa yankin Kudu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Magauta sun yi hayar makasa, sun hallaka jigon APC mai fada a ji a wata jiha

Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ne ake cewa yana kokarin rusa shirin da ake yi, ya kuma hada-kai da ‘yan majalisar NEC domin a takawa G5 burki.

A yayin da Sanata Bala Mohammed yake neman shawo kan ‘yan majalisar kolin PDP, an yi wani taron G5 a garin Fatakwal a karshen makon da ya gabata.

Wike bai tare da PDP a zaben majalisa

'Yan PDP, NNPP da LP da za su je majalisa a bana, za su yaki APC a zaben da za ayi, rahoto ya zo cewa Gwamnan Jihar Ribas ya janye jikinsa daga tuggun.

Gwamna Nyesom Wike ya ce 'yan majalisan Ribas ba za su goyi bayan shirin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel