“Ba Wasa Muke Yi a Nan Ba”: Gwamna Wike Ya Wofantar Da Kudirin Takarar Gwamnan Dino Melaye

“Ba Wasa Muke Yi a Nan Ba”: Gwamna Wike Ya Wofantar Da Kudirin Takarar Gwamnan Dino Melaye

  • Gwamna Nyesom Wike ya yi watsi da yiwuwar Sanata Dino Melaye ya lashe tikitin PDP na zaben gwamnan Kogi
  • Gwamnan na jihar Ribas ya ce jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi za ta yi babban kuskure idan suka tsayar da Sanata Melaye
  • Ya bayyana cewa PDP ba za ta samu goyon bayansa ba idan har tikitin takarar gwamnan jam'iyyar ya shiga hannun Melaye

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya gargadi jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Kogi cewa suna shirin faduwa zaben gwamnan 2023 idan har suka mika tikitin jam'iyyar ga Sanata Dino Melaye.

A yan makonnin da suka gabata, Dino ya sanar da kudirinsa na son takarar kujera ta daya a jihar Kogi.

Gwamna Nyesom Wike da Sanata Dino Melaye
“Ba Wasa Muke Yi a Nan Ba”: Gwamna Wike Ya Wofantar Da Kudirin Takarar Gwamnan Dino Melaye Hoto: Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON, Dino Melaye
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa yayin wata tattaunawa da manema labarai a Port Harcourt a ranar Talata, 11 ga watan Afrilu, Gwamna Wike, ya ce Sanata Melaye bai da abun da ake bukata don shugabantar wata jiha.

Kara karanta wannan

An samu matsala: Jam'iyyar APC ta kori wani fitaccen sanata a jihar Arewa

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Me zai sa mutanen Kogi su ce za su zabi dan takara kamar Dino? Shin wasa muke yi? Idan kuka ba Dino tikitin nan, ku san cewa ba zai yi nasara ba a jihar Kogi.
"Dino bai da abun da ake bukata don zama gwamna saboda Allah. Ya san ni sosai. Bai da abun da ake bukata don zama gwamna."

A cewar Channels TV, Gwamna Wike ya bayyana cewa yankin da Melaye ya fito ba tabbaci bane na cewa zai yi nasara a zaben.

Ya ce PDP reshen jihar Kogi za su harbi kansu a kafa idan har suka mika tikitin takarar gwamna gare shi.

Gwamna Wike ya ce:

"Shin hakan na nufin cewa idan PDP na son lashe zabe, sai ta baiwa Dino tikitinta sannan gobe ku je an yi maku magudi a zabe alhalin kun rigada kun kashe kanku?"

Kara karanta wannan

“Kasuwa Bata Yi Mun Dadi Ba”: Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Faduwa Da Ya Yi a Zaben Sanata

"Shin muna so mu ce muna son lashe zabe ne ko kuma kawai mu kasance da dan takara?"

Ba zan yi wa PDP kamfen ba idan Dino ya lashe tikitin gwamna - Gwamna Wike

Da aka tambaye shi ko zai kasance tare da PDP idan Sanata Melaye ya lashe tikitin gwamna, Gwamna Wike ya ce 'a'a' kuma cewa ba zai yi wa yan adawa kamfen ba.

Ya ce:

"Kuna bukatar yi mani irin wannan tambaya? Ba ku san cewa ba zan aikata haka ba?"

Jerin yan PDP 5 da ke hararar kujerar Yahaya Bello

A gefe guda, mun ji cewa akwai wasu manyan yan siyasa na PDP guda biyar wadanda sune kan gaba cikin masu neman tikitin jam'iyyar domin darewa kujerar gwamnan jihar Kogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel