Zaben 2023: Atiku, Obi Da Sauran Yan Takarar Da Ke Kalubalantar Nasarar Tinubu a Kotu

Zaben 2023: Atiku, Obi Da Sauran Yan Takarar Da Ke Kalubalantar Nasarar Tinubu a Kotu

Bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu wanda ya samar da dan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, a matsayin zababben shugaban kasa, ana ta samun koke-koke daga jam'iyyun siyasa.

A halin yanzu, jam'iyyun siyasa 4 daga cikin 18 da suka fafata a zaben sun dauki matakin shiga kotu don nuna adawa ga sanarwar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC).

Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Peter Obi kowannensu na jawabi
Zaben 2023: Atiku, Obi Da Sauran Yan Takarar Da Ke Kalubalantar Nasarar Tinubu a Kotu Hoto: @atiku/@officialABA/@PeterObi
Asali: Twitter

A ranar Talata, 21 ga watan Maris, masu karar sun nemi a soke zaben da ya samar da Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben.

Ga jerin yan takarar da suka shigar da kara

  1. Atiku Abubakar, na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP)
  2. Peter Obi, jam'iyyar Labour Party (LP)
  3. Solomon Okangbuan, jam'iyyar Action Alliance (AA)
  4. Chichi Ojei, jam'iyyar Allied People’s Movement (APM)

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Hotuna Sun Bayyana Yayin da Zanga-Zanga Ke Gudana a Ofishin INEC Kan Ayyana Sakamakon Zaben Gwamna a Wata Jiha

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kara daban-daban masu lamba CA/PEPC/03/2023; CA/PEPC/01/2023; da CA/PEPC/04/2023, yan takarar shugaban kasar suna kalubalantar sakamakon zaben saboda rashin bin tsarin dokar zabe.

Suna kuma zargin cewa wanda ya lashe zaben bai bi tsarin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ba.

Masu karar sun kuma garzaya kotu ne saboda zargin rashin bin ka'ida da magudin zabe yayin da INEC ta gaza daura sakamakon zaben a shafinta na IREV daga rumfunan zabe.

A karar tasu, INEC ce mutum na farko da ake kara yayin da Tinubu, zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da APC suka kasance na biyu, uku da hudu.

Ba zan taba komawa jam'iyyar APC, Fayose

A gefe guda, tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya yi watsi da rade-radin da ake yi na cewa yana gab da komawa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: APC Ta Kwace Mulki Daga PDP, Babban Malami Ya Lashe Zaben Gwamna a Jihar Arewa

An dai fara hasashen komawar Fayose APC ne tun bayan da ya fito karara ya nuna goyon bayansa ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu tun kafin zaben 2023 sannan ya yi watsi da dan takarar jam'iyyarsa, Atiku Abubakar.

Sai dai duk da rade-radin, Fayose ya ce sam ba zai koma APC ba asalima ya ce ya marawa Tinubu baya ne saboda yana ganin akwai bukatar mulki ya koma yankin kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel