Ogun 2023: Ana Zanga-Zanga a Ofishin INEC Don Kalubalantar Nasarar Gwamna Abiodun

Ogun 2023: Ana Zanga-Zanga a Ofishin INEC Don Kalubalantar Nasarar Gwamna Abiodun

  • Ana kalubalantar nasarar Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun a zaben gwamnan 2023 da aka kammala
  • Masu zanga-zanga sun mamaye ofishin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a Abeokuta don neman a ayyana zaben a matsayin ba kammalalle ba
  • Hakazalika, jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta roki INEC da ta yi duba ga tsarin tazara tsakanin wadanda ke gaba

Ogun - Dan takarar gwamnan jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) a zaben jihar Ogun da aka kammala, Ladi Adebutu, ya jagoranci masu zanga-zanga zuwa ofishin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC).

Hakan na zuwa ne kasa da awa 24 bayan hukumar INEC ta ayyana gwamna mai ci, Dapo Abiodun na jam'iyyar All Progressive Congress (APC), a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan 2023 a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

2023: Jerin Jihohin da Ba'a Kammala Zaben Gwamna Ba da Waɗanda INEC Ta Dakatar da Tattara Sakamako

Jama'a na gudanar da zanga-zanga a Ogun
Ogun 2023: Ana Zanga-Zanga a Ofishin INEC Don Kalubalantar Nasarar Gwamna Abiodun Hoto: Ladi Adebutu Support Group
Asali: Facebook

Kayode Adebowale, baturen zabe a jihar Ogun, ya ce gwamna mai ci ya samu kuri'u 276,298 wajen yin nasara a kan Adebutu na PDP wanda ya samu kuri'u 262,383 a zaben.

Masana harkokin siyasa da masu kishin kasa da suka soki tsarin zaben da ya kai ga zarcewarsa sun bayyana nasarar Gwamna Abiodun a matsayin tsallake rijiya da baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin da ake ciki, PDP ta rigada ta fara daukar matakai don tabbatar da ganin an ayyana zaben a matsayin ba kammalalle ba.

Legit.ng ta kawo da farko cewa, sakataren jam'iyyar a jihar, Sunday Solarin, ya aika rkokensu ga INEC a jihar Ogun sannan ya aika ga shugaban hukumar na kasa, Mahmood Yakubu.

Zaben gwamna: Jami'an tsaro sun zama cikin shirin ko-ta-kwana a jihar Kaduna

A wani labari nna daban, gwamnatin jihar Kaduna ta jaddada matsayinta da ke haramta yin zanga-zanga da gangamin siyasa a jihar don tabbatar da doka da oda.

Kara karanta wannan

Wasu ‘Yan Takaran APC Za Su Kotu Domin Karbe Nasarar PDP a Zaben Gwamnoni

Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya bayyana cewa jami'an tsaro a jihar sun kasance cikin shiri don tabbatar da ganin wani ko kungoyoyi basu ta da zaune tsaye ba bayan zaben gwamnoni da aka yi.

Ya bayyana cewa sun samu wani bayanai na sirri na kulle-kullen da wasu ke yi don haddasa rikici a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel