“Na Marawa Tinubu Baya Amma Ba Zan Taba Zama Dan APC Ba” – Inji Fayose

“Na Marawa Tinubu Baya Amma Ba Zan Taba Zama Dan APC Ba” – Inji Fayose

  • Ayo Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya jaddada cewa baya tunanin komawa jam'iyyar APC
  • Fayose ya yi karin hasken ne bayan ya marawa Tinubu baya a kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa, Atiku Abubakar
  • Jigon na PDP ya ce burinsa ya cika bayan ya yi aiki a matsayin gwamna a jiharsa na tsawon wa'adi biyu

Lagos - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana cewa ba zai taba komawa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ba duk da ya fito karara ya nuna goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Bola Tinubu kafin zaben 2023.

Fayose ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Talata, 21 ga watan Maris, yan kwanaki bayan zaben 2023.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Katsina: PDP Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Bayan Shan Kaye

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose
“Na Marawa Tinubu Baya Amma Ba Zan Taba Zama Dan APC Ba” – Inji Fayose Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Fayose, wanda ya yi adawa da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyarsa ta PDP, Atiku Abubakar ya ce ya marawa Tinubu baya ne saboda ya yarda cewa ya kamata mulki ya koma yankin kudu.

Kalamansa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"An sha tunkarar mutane da dama a Najeriya kan abun da suka fadi a lokuta mabanbanta, kuma imma su jaddada ko su fadi sabon abu. Ni gani na tsaya a nan don fada maku cewa ba zan taba zama dan APC ba.
"A yanzu bana siyasa kan abun da yake kuma. An bani dama sau biyu don jagorantar Ekiti kuma na kayar da gwamnoni masu ci guda biyu."

Ya shawarci mambobin jam'iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP) da su dinke barakarsu sannan su yi aiki gabannin zaben 2027 idan suna son karbar mulki, rahoton Punch.

Ya kuma gargadi shugabanni a kasar da su gyara zama, cewa lamarin da ya kai ga zaben 2023 da ra'ayin da matasa suka nuna ya nuna cewa a yanzu ba kasuwanci bane kamar da.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC Ya Sha Da Ƙyar, Ya Lashe Zaben Gwamna a Jiharsa

Ku ayyana sakamakon zaben gwamnonin Abia da Enugu - Obi ga INEC

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya bukaci hukumar zabe ta kasa (INEC) da ta sanar da sakamakon zaben gwamnonin jihar Abia da Enugu ba tare da bata lokaci ba.

A cewar Obi, rashin yin hakan zai dasa ayar tambaya a kan sahihanci da kudirin hukumar zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel