APC Ta San Makomar ta, An Sanar da Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna a Nasarawa

APC Ta San Makomar ta, An Sanar da Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna a Nasarawa

  • Abdullahi A. Sule ya yi nasara a zaben Gwamnan Jihar Nasarawa da aka shirya a makon jiya
  • Gwamnan zai cigaba da mulki zuwa watan Mayun 2023 bayan ya yi galaba a kan Jam’iyyar PDP
  • Burin David Ombugadu na zama Gwamna bai tabbata, PDP ta nuna za ta shigar da kara a kotu

Nasarawa - A ranar Litinin, 20 ga watan Maris 2023, hukumar INEC ta tabbatar da cewa Gwamna Abdullahi A. Sule zai zarce a kan kujerarsa.

Rahoton tashar talabijin na Channels ya tabbatar da cewa Mai girma Abdullahi A. Sule ya yi nasara a jam’iyyar APC a zaben Gwamna da aka yi.

Baturen zaben Gwamna a Nasarawa, Farfesa Tanko Ishaya ya ayyana jam’iyyar APC a matsayin wanda ta lashe zaben bana da kuri’u 347, 209.

Kara karanta wannan

Zaben Gwamna: Hukumar INEC Ta Sanar da ‘Inconclusive’ a Kebbi

Wanda ya zo na biyu a zaben shi ne David Ombugadu na jam’iyyar PDP da ya samu kuri’u 283,016.

Nasarawa
APC a Nasarawa Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kotu za ta raba gardama

Rahoton ya ce amma jam’iyyar hamayya ta PDP ta nuna ba ta ji dadin sakamakon da aka sanar ba, ta shaida cewa za ta shigar da kara a kotun zabe.

Haka zalika APC da tayi nasara a zaben na ranar Asabar, ta ce za ta shigar da kara a kotu, ta kalubalanci nasarar da PDP ta samu a wasu wurare.

Sule ya gagari 'Yan adawa

The Guardian ta ce a zaben 2019, David Ombugadu ya gwabza da A. A Sule, amma bai kai labari ba. A wancan lokci PDP ta samu kuri’u 184, 281 ne.

Wannan karo ‘dan takaran PDP ya hada kai da tsohon Minista, Labaran Maku wanda yake neman mulki a APGA domin a kifar da gwamnatin APC.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Jam'iyyar PDP Ta Lashe Zaben Gwamnan Jihar Oyo

Sau biyu a jere kenan Injiniya Sule yana Ombugadu a zaben Gwamna a jihar Nasarawa.

Zaben Jihar Legas

An samu labari mutane 1,182,620 aka tantance a zaben, a ciki kusan 65% sun zabi Jam'iyyar APC, Gwamna Babajide Sanwo Olu zai zarce a mulki.

Gbadebo Rhodes-Vivour ya yi nasara a karamar hukuma daya ne rak, yana da kuri'u 312,329 sai kuma 'dan takaran jam'iyyar PDP ya ci kuri'u 64, 000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel