Jihohin da INEC Ta Ayyana Zaben Gwamna da Bai Kammalu ko Ta Dakatar da Haɗa Sakamako

Jihohin da INEC Ta Ayyana Zaben Gwamna da Bai Kammalu ko Ta Dakatar da Haɗa Sakamako

Kawo yanzun kowane ɗan takara ya san makomarsa a zaben gwamnonin da ya gudana ranar Asabar 18 ga watan Maris, 2023, a jihohi 24 cikin 28.

Zaben ya zo da abubuwan ban mamaki da ba'a yi tsammani ba. A jihar Kano, ɗan takarar gwamna karkashi inuwar NNPP mai kayan marmari ya samu nasara mai tarihi kan APC mai mulki.

Amma a wasu jihohin kuma sakamakon ya zo kamar yadda aka yi hasashe zai faru bayan la'akari da masu neman takara da jam'iyyun da suka ba su tikiti.

Zauren tattara sakamako.
Jihohin da INEC Ta Ayyana Zaben Gwamna da Bai Kammalu ko Ta Dakatar da Haɗa Sakamako Hoto: Nnenna Ibe
Asali: Original

Sai dai akwai wasu jihohi kalilan, waɗanda hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta yanke hukunci mai tsauri saboda da ba ta da wani zaɓi illa haka duba da abinda ya faru.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku jihohin da INEC ta tsoma baki da kuma waɗanda ta ayyana zaben gwamna da bai kammalu ba kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Buri ya cika: Daga cin zabe, sabon gwamnan Sokotomya fadi abubuwa 9 da zai yi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jerin jihohin da INEC ta ayyana zabe da 'Inconclusive' watau bai kammalu ba

1. Jihar Adamawa (Shiyyar arewa maso gabashin Najeriya)

2. Jihar Kebbi (Shiyyar arewa maso yammacin Najeriya).

Doka ta baiwa INEC ikon ayyana zabe a matsayin wanda bai kammalu idan har an samu rumfunan da aka soke zabe suna da adadin masu kaɗa kuri'a fiye da tazarar da ke tsakanin na ɗaya da na biyu.

Irin haka ne ta faru a Adamawa tsakanin gwamna mai ci, Ahmadu Fintiri, da kuma yar takarar APC, Sanata Aishatu Binani. Zaben ya ja hankalin mutane daga ciki da wajen Najeriya.

Jerin jihohin da INEC ta dakatar da zabe da tattara sakamako

1. Jihar Abiya (kudu maso gabashin Najeriya)

2. Jihar Enugu (kudu maso gabashin Najeriya).

Zaben wannan jihohin cike yake da rikici da ta da yamutsi, lamarin da ya tilasta wa INEC ɗaukar mataki mai tsauri.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC Ya Sha Da Ƙyar, Ya Lashe Zaben Gwamna a Jiharsa

A wani labarin kuma mun zakulo muku Jerin Sunayen Sabbin Gwamnoni da Aka Zaba Zangon Farko, Jam'iyyu da Jihohinsu

Bayan gama zaben gwaamnoni a Najeriya, jihohi sun samu sabbin shugabanni yayin da wasu kuma suka zabi gwamnoni masu ci su ci gaba da mulki.

Mun haɗa maku jerin jihohi 14 da mutane suka zabi sabbin gwamnoni, waɗanda zasu fara mulki a karon farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262