Amaechi Ya Na Zargin Magudi, Ya Tona Yadda Farfesa Yakubu Ya Zama Shugaban INEC

Amaechi Ya Na Zargin Magudi, Ya Tona Yadda Farfesa Yakubu Ya Zama Shugaban INEC

  • Rotimi Amaechi yana zargin Shugaban INEC ya hada-kai da Gwamnan Ribas wajen murde zabe
  • Tsohon Ministan sufuri ya ce mutanensu Bola Tinubu suka yi wa Mahmud Yakubu hanyar tazarce
  • Amaechi ya yi ikirarin Shugaban na INEC ya yi a karkashin Nyesom Wike a sa’ilin da yake TETFund

Rivers - Tsohon Ministan sufuri a Najeriya, Rotimi Amaechi ya zargi shugaban hukumar zabe na kasa, Farfesa Mahmud Yakubu da rashin adalci a zabe.

A ranar Asabar tashar talabijin Arise ta rahoto Rotimi Amaechi yana cewa mutanen Bola Tinubu suka taimaka Mahmud Yakubu ya samu karin wa’adi a ofis.

A cewar tsohon Ministan, a lokacin da wa’adin Farfesa Yakubu ya cika, daga bangaren Tinubu aka samu wanda ya bada sunansa domin a kara nada shi.

Bayan kada kuri’arsa a mazabarsa da ke Ubima a Ribas a jiya, Amaechi ya nuna rashin jin dadinsa a kan yadda abubuwa suke tafiya a zaben Gwamnoni.

Kara karanta wannan

'Dan takaran Sanatan APC a Kaduna Zai Tafi Kotu, Ya Fito da Hujjojin Magudin PDP

Amaechi: Da INEC muke takara

‘Dan siyasar ya yi ikirarin cewa jam’iyyarsa ta APC ba da PDP tayi takara ba, ya ce jami’an ‘yan sanda da INEC su na cikin abokan adawarsu a zaben.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard ta rahoto Amaechi wanda ya yi Gwamna sau biyu a Ribas yana cewa shugabanci ya lalace domin ana amfani da ‘yan sanda wajen barna.

Amaechi da Buhari
Amaechi da Shugaban Kasa Hoto: punchng.com
Asali: UGC

"Sha’anin shugabanci ya tabarbare gaba daya. ‘Yan sanda su na taimakawa jam’iyyar PDP wajen cafke ‘yan APC da SDP.
‘Yan dabar siyasa su na dirkar mutane cewa dole su fito su zabi PDP. Ana doke PDP, Gwamna ya fito yana cewa a cafke wasu.
Babu wanda zai iya fitowa domin ana tsoro. INEC ta bada kunya, shiyasa muka yi adawa da sake nada Yakubu Mahmood.
Wanda ya bada sunan shi ‘dan gidan Tinubu ne, saboda haka me ku ke tunanin zai faru?"

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Shiga Neman Tsohon Gwamna Kan ‘Kisan Kai da Garkuwa da Mutane’

- Rotimi Amaechi

A cewar jigon na APC, Wike yana da alaka da Shugaban hukumar zabe, ya ce lokacin da Farfesa Yakubu yake TETFund, Gwamnan ya yi Ministan ilmi.

Sakamako sun fara fitowa

Zuwa yanzu wasu sakamakon sun fito daga irinsu Kaduna, Bauchi, Legas, Oyo zuwa Jihar Kano, mun tattaro maku manyan labarai a wannan rahoto.

A zaben Benuwai, ‘Dan takaran APC, Rabaren Hyacinth Alia ya doke PDP a gidan Gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel