‘Yan Sanda Sun Shiga Neman Tsohon Gwamna Kan ‘Kisan Kai da Garkuwa da Mutane’

‘Yan Sanda Sun Shiga Neman Tsohon Gwamna Kan ‘Kisan Kai da Garkuwa da Mutane’

  • A jihar Imo, an bukaci PDP ta fito da Emeka Ihedioha, Ugochinyere Ikenga da Gerald Irona
  • Jami’an ‘yan sanda su na zargin wadannan manyan ‘yan siyasa da hannu wajen kashe-kashe
  • Jam’iyyar PDP ta nesanta kan ta daga zargin, ta ce shirin APC ne na murde zabe mai zuwa

Imo - Jami’an ‘yan sanda a jihar Imo sun gayyaci Emeka Ihedioha da Ikenga Ugochinyere bisa zargin kisa, satar mutane da cinnawa gini wuta.

Tashar talabijin Channels TV ta rahoto cewa ‘yan sanda sun aika goron gayatta zuwa manyan 'yan siyasar na Imo domin su samu damar wanke kan su.

Ikenga Ugochinyere, daya daga cikin wadanda ake tuhuma shi ne Kakakin kungiyar CUPP. Ana kuma neman tsohon Mataimakin gwamna a jihar Kudun.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Imo, Ahmed Barde ya aika takardar gayyatar wadannan mutane zuwa ga shugaban PDP watau Mr. Charles Ugwu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kama Mataimakin Shugaban APC Na Jiha Kwana 2 Gabanin Zabe

Wasikar DCP Ukachi Opara

Wannan takarda da ta fito ta ranar 13 ga watan Maris 2022 ta samu sa hannun Kwamishinan gudanarwa na ‘yan sanda, DCP Ukachi Opara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya ce DCP Opara ya bukaci Ugwu ya fito da jagororin jam’iyyarsa a ranar Alhamis, ya kai su babban ofishin bincikensu da yake Owerri.

‘Yan Sanda
Rundunar 'Yan Sanda Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Mutane uku da ake nema su ne tsohon shugaban majalisar wakilai, mai magana da yawun CUPP, da tsohon mataimakin Gwamna, Gerald Irona.

Martanin PDP da 'yan sanda

Kwamishinan ‘yan sanda ya bukaci ka zo da wadannan mutane Emeka Ihedioha, Ugochinyere Ikenga da Gerald Irona domin yi masu tambayoyi.

Kakakin jami’an tsaro, Henry Okoye ya shaidawa jaridar Premium Times cewa babu shakka wannan takarda daga hannun ‘yan sandan Imo ya fito.

Amma duk abin da yake faruwa, Charles Ugwu ya bayyana cewa a kafafen sada zumunta ya ga takardar, ya na nufin ‘yan sanda ba su tuntube shi ba.

Kara karanta wannan

Kano, Kaduna da Jihohi 10 da Sai Gwamnoni, ‘Yan Takara Sun Yi Da Gaske a Zaben 2023

Mai magana da yawun bakin PDP a Imo, Collins Opurozor ya na zargin Gwamna Hope Uzodinma ya shirya wannan saboda a murde zaben Jihar.

Jam’iyyar hamayya ta PDP ta bukaci Sufeta Janar na ‘Yan Sanda ya tsige CP Ahmed Barde.

An kama 'Dan shekara 36

Idan za ku iya tunawa, a makon nan aka samu rahoto cewa Rundunar 'Yan sandan Legas sun yi ram da wani mai shekara 36 da zargi mai ban al'ajabi.

Lauyan 'yan sanda ya fadawa Kotu cewa Innocent Osanebi ya aukawa mahaifinsa da wuka tsirara. Abin ya faru ne a unguwar Ojodu Berger a jihar Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel