Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Ekiti, Egbeyemi, Ya Kwanta Dama

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Ekiti, Egbeyemi, Ya Kwanta Dama

  • Tsohon mataimakin gwannan jihar Ekiti wanda ya sauka a bara 2022, Bisi Egbeyemi, ya riga mu gidan gaskiya
  • Bayanai sun nuna cewa marigayin ya rasu ne bayan fama da wata gajeruwar rashin lafiya a Aso-Ekiti, babban birnin jiha
  • Wata majiya ta ce nan gaba kaɗan za'a ji sanarwa a hukumance daga bakin gwamnatin jihar Ekiti kan wannan rashin

Ekiti - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Ekiti da ya sauka, Bisi Egbeyemi, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 78 a duniya.

Jaridar Punch ta tattaro cewa Mista Egbeyemi ya rike kujerar mataimakin gwamna a lokacin mulkin gwamna Kayode Fayemi. Ya yi aiki a tsakanin 2018 zuwa 2022.

Bisi Egbeyemi.
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Ekiti, Egbeyemi, Ya Kwanta Dama Hoto: punchng
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa tsohon mataimakin gwamnan ya rasu ne da kusan misalin karfe 8:00 na daren ranar Jumu'a bayan fama da yar gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC Ta Lallasa PDP A Cikin Gidan Gwamnati Na Ortom

Bugu da ƙari, an tattro cewa Marigayin ya cika ne a wani Asbitin kuɗi da ke Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar Ekiti kawo yanzu amma wata majiya da ke kusa da tsohon gwamnan ta tabbatar da rasuwarsa ga Premium Times ta rahoto.

"Eh, da gaske ne, tsohon mataimakin gwamna ya riga mu gidan gaskiya," inji majiyar wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda ba shi da hurumin tsoma baki kan lamarin.

"Kafin yammacin yau sanarwa zata hito daga gwamnati a hukumance."

Bayan haka, Mista Segun Dipe, jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar APC mai mulki ya tabbatar da rasuwan tsohon mataimakin gwamna.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa rasuwar jigon siyasa na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya suka koma rumfunan zabe domin zakulo gwamnoni a yan majalisar jihohi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Yi Dirama Yayin Da Biri Ya Iso Rumfar Zabe Ya Tarwatsa Masu Kada Kuri'a A Kano

A jihar Ekiti, zaben mambobin majalisar dokoki kaɗai aka gudanar sakamakon ba'a jima da gudanar da zaben gwamna ba.

Jam'iyyar PDP Ta Lallasa APC a Gidan Gwamnatin Malam El-Rufai

A.wani labarin na daban kuma Jam'iyyar PDP ta samu galaba a rumfunan zabe 2 da ke cikin gidan gwamnatin jihar Kaduna

PDP ta samu nasara a rumfunan zabe 2 na gidan gwamnatin El-Rufai, Isah Ashiru Kudan ya lallasa Uba Sani a PU 013 da 014.

Asali: Legit.ng

Online view pixel