Wasu Kungiyoyin Matasa Sun Nuna Goyon Bayan Su Ga Takarar Uba Sani a Kaduna

Wasu Kungiyoyin Matasa Sun Nuna Goyon Bayan Su Ga Takarar Uba Sani a Kaduna

  • Wasu ƙungiyoyi biyu a Kudancin Kaduna sun nuna goyon bayan su ga ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar APC
  • Ƙingiyoyin biyu sun bayyana cewa za su yi duk mai yiwuwa domin ganin ɗan takarar ya samu nasara a zaɓen mai zuwa
  • Sun kuma nuna ƙwarin guiwar su kan cewa ɗan takarar zai gyara kura-kuran gwamnan jihar Nasir El-Rufai

Jihar Kaduna- Ƙungiyoyin Southern Kaduna People’s Union (SOKAPU) ɓangaren matasa da Southern Kaduna Youth and Students Forum (SKYSFOM) sun nuna goyon bayan su ga ɗan takarar gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Sanata Uba Sani.

Ƙungiyoyin biyu sun bayar da tabbacin cewa ɗan takarar gwamnan na jam'iyyar APC zai gyara dukkanin kura-kuran gwamna Nasir El-Rufai, idan aka zaɓe shi. Rahoton The Nation.

Uba Sani
Wasu Kungiyoyin Matasa Sun Nuna Goyon Bayan Su Ga Takarar Uba Sani a Kaduna
Asali: Facebook

A wata takardar haɗin guiwa da shugaban SKYSFOM, Ernest Maidawa da kodinetan SOKAPU ɓangaren matasa na ƙasa, Luke Augustine Gwazah, suka fitar, sun bayyana cewa sun shirya tsaf domin bada gudunmawar su wajen samun nasarar Uba Sani.

Sun bayyana za su shiga lungu da saƙo domin tatttaro matasan Kudancin Kaduna domin tabbatar da cewa sun yiwa Uba Sani ruwan ƙuri'u a zaɓen gobe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani ɓangare na takardar na cewa:

“Bayan lura da idon basira, mu matasan Kudancin Kaduna a ƙarƙashin ƙungiyar Southern Kaduna Youth and Students Forum -SKYSFOM da ɓangaren matasan ƙungiyar The Southern Kaduna People’s Union (SOKAPU) mun amince mu marawa Uba Sani baya a zaɓen gwamnan ranar Asabar.
"Mun yanke wannan hukuncin ne bisa la'akari da ɗumbin nasarorin da ya samu yana Sanata a majalisar dattawa da kuma yadda yake yanke hukunci bisa ƙashin kansa ba tare da tsoro ko fargaba abinda ka iya biyo baya ba."
“Muna da ƙwarin guiwar cewa Sanata Uba Sani ba zai zama irin gwamnan da ya gabace shi ba idan aka zaɓe shi a zaɓen ranar Asabar."

Ko a baya dai Sanata Uba Sani yasha bayyana cewa zai sauya wasu tsare-tsare na gwamnatin El-Rufai idan ya hau mulki. Rahoton Daily Trust

Gwamna Kwara Ya Samu Tagomashi Dan Takarar Gwamna Ya Janye Masa Takara

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Kwara na jam'iyyar APC ya samu babban tagomashi ana dab da zabe.

Wani ɗan takarar gwamna a jihar yace ya haƙura ya janye masa takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel