LP Da NNPP Sun Cure Wuri Daya da APC Domin Ganin Bayan PDP a Neja

LP Da NNPP Sun Cure Wuri Daya da APC Domin Ganin Bayan PDP a Neja

  • Kwana 2 gabanin zaben gwamna, jam'iyyar APC ta samu babban goyon baya da ga manyan jam'iyyu biyu a jihar Neja
  • Labour Party da kuma New Nigerian People Party sun haɗa kai, sun koma bayan ɗan takarar gwamnan APC, Umar Bago
  • Mista Bago, ya ce idan har ya kafa gwamnati, zai yi aiki hannu da hannu da LP da NNPP

Niger - Ƙasa da awanni 48 gabanin zaben gwamnoni da mambobin majalisar dokoki wanda zai gudana ranar 18 ga watan Maris, 2023, jam'iyyu sun ci gaba kulla kawance don samun nasara.

Bisa haka, shugabannin Labour Party da NNPP mai kayan marmari a jihar Neja sun cure wuri ɗaya, sun marawa ɗan takarar gwamnan APC, Umar Bago, baya.

Umar Bago.
Dan takarar gwamnan APC a Neja, Umar Bago Hoto: Umar Bago
Asali: UGC

Rahoton Channels tv ya tattaro manyan jam'iyyun biyu na cewa ɗan takarar ne kaɗai ya shirya tsaf kuma yana da gogewar da ake bukata domin kafa gwamnati mai kyau.

Kara karanta wannan

Jerin 'Yan Takarar Gwamna 3 da Aka Raina Kuma Zasu Iya Ba Da Mamaki a Zaben Gwamnoni

Sun bayyana wannan matakin ne a jawabin da suka yi daban-daban daga bakin shugaban LP, Musa Mohammed da Sakataren jam'iyyar NNPP, Mohammed Kwabo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bugu da ƙari, shugabannin jam'iyyun biyu sun kara da bayanin cewa wannan matakin da suka ɗauka na goyon bayan APC ba kuɗi ne suka ruɗe su ba, sun yi haka ne domin kishin jihar Neja.

Ɗan takarar gwamnan APC, Umar Bago, ne ya tarbi shugabannin LP da NNPP tare da ɗumbin mambobinsu hannu bibbiyu.

Ya tabbatar musu da cewa zasu yi aiki kafaɗa da kafaɗa domin inganta jihar idan har Allah ya ba shi nasarar zama gwamna a zaben ranar Asabar, kamar yadda Thisday ta rahoto.

Tun da zaben ya ƙara matsowa, jam'iyyu da dama sun haɗe da wasu a jihohi daban-daban, wasu sun ware wasu kuma sun kulla kawance duk da nufin tunkarar zabe ranar 18 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

2023: An Samu Matsala, Jam'iyya Ta Dakatar da Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Arewa Kwana 4 Gabanin Zabe

IGP Ya Umarci a Takaita Zirga-Zirga

A wani labarin kuma IGP Ya Umarci a Takaita Zirga-Zirgan Ababen Hawa Ranar Zaben Gwamnoni Mai zuwa

Shugaban rundunar yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya ba da umarnin cewa babu zirga-zirgan ababen hawa a faɗin ƙasa nan ranar Asabar 18 ga watan Maris.

A wata sanarwa da rundunar 'yan sanda ta fitar yau Alhamis, ta ce babu yawon ababen hawa daga tsakar daren Jumu'a har zuwa 6:00 na yammacin Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel