Ana Dab da Zabe, LP Ta Dakatar da Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Kwara

Ana Dab da Zabe, LP Ta Dakatar da Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Kwara

  • Jam'iyyar LP ta dakatar da ɗan takarar gwamna a jihar Kwara, Basambo Abubakar, kwana 4 gabanin zabe
  • Shugaban LP, Kehinde Rotimi, ya ce jam'iyyar ba ta kulla kwance da kowane ɗan takara ko jam'iyyar siyasa ba
  • LP ta dauki wannan matakin ne bayan ɗan takarar ya ce sun kulla ƙawance da PDP, lamarin da shugabanni suka ƙaryata

Kwara - Jam'iyyar Labour Party reshen jihar Kwara ta sanar da dakatar da ɗan takararta na gwamna, Basambo Abubakar, har sai baba ta gani.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa LP ta ɗauki wannan matakin kan ɗan takarar ne bisa zargin zagon ƙasa da kuma yaɗa bayanan ƙarya da sunan jam'iyyar.

Dan takarar LP a Kwara.
Ana Dab da Zabe, LP Ta Dakatar da Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Kwara Hoto: thenationonlineng
Asali: UGC

Wannan ci gaban ya zo kwanaki huɗu gabanin zaben gwamna da mambobin majalisar dokokin jiha wanda zai gudana ranar Asabar 18 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

APC Na Tsaka Mai Wuya, Ɗan Takarar Gwamna Ya Janye Daga Takara Kwana 4 Gabanin Zabe

A ranar Litinin da ta gabata, Kwamaret Abubakar, ya ce LP da jam'iyyar PDP sun cimma matsayar aiki tare a zaben gwamnan da ke tafe a Kwara, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abubakar, tsohon hadimin tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya ce wannan kawance da suka kulla zai samar da kyakkyawa kuma ingantacciyar jihar Kwara.

Shin dagaske LP ta haɗa kai da PDP?

Da yake jawabi ga yan jarida a Ilorin, shugaban LP, Kwamaret Kehinde Rotimi, ya ce jam'iyyar ba ta haɗa kawance da kowane ɗan takarar gwamna ko wata jam'iyar siyasa ba.

Ya ce dakataccen ɗan takarar gwamnan a inuwar LP ya aikata haka ne da nufin yaƙar abinda jam'iyyar ta tsaya a kansa. A cewarsa ba shi da hurumin sanar da batun haɗan kan LP da wata jam'iyya.

Kara karanta wannan

Bayan Sauya Naira, Emefiele Ya Sake Bullo da Sabuwar Hanyar Yaƙar Tinubu? CBN Ya Fitar da Sanarwa

Sakamakon haka shugaban LP na Kwara ya bukaci ɗaukacin al'umma su yi fatali da kalaman ɗan takarar gwamnan, "Dukkan yan takarar LP na majalisar dokoki na cikin tsere, muna rokon mutane su zaɓi LP ranar Asabar."

Dan Takarar Gwamnan Oyo Na SDP Ya Janyewa Gwamna Makinde

A wani labarin kuma Mai neman zama gwamnan Oyo a inuwar SDP ya hakura da takara, ya koma bayan gwamna Makinde na PDP

Mista Michael Lana, ya ce gwamna Makinde na neman taimako a kudirinsa na nemnan tazarce ranar zaben gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel