IGP Ya Umarci a Takaita Zirga-Zirgan Ababen Hawa Tanar Zaben Gwamnoni

IGP Ya Umarci a Takaita Zirga-Zirgan Ababen Hawa Tanar Zaben Gwamnoni

  • IGP Usman Alkali Baba ya haramta zirga-zirgan ababen hawa a ranar zaben gwamnoni da yan majalisun jihohi
  • A wata sanarwa da kakakin rundunar yan sanda ya fitar, ya ce dokar zata fara aiki da tsakar dare har zuwa 6:00 na yammacin Asabar
  • Sufetan yan sanda ya yi kira ga ɗaukacin 'yan Najeriya su zama masu ɗa'a da bin doka a lokacin zabe da kuma bayan an gama

Abuja - Sufeta janar na rundunar 'yan sandan Najeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya umarci a taƙaita zirga-zirgan motoci da sauran ababen hawa lokacin zaben gwamnaoni da 'yan majalisar dokoki.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan ƙasar nan, Muyiwa Adejobi, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 16 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnatin Tarayya Ta Tsayar Da Sabon Lokacin Kidaya Yan Najeriya

Babban Titi a Najeriya.
IGP Ya Umarci a Takaita Zirga-Zirgan Ababen Hawa Tanar Zaben Gwamnoni Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Ya ce dokar takaita zirga-zirgan ababen hawan zata fara aiki ne daga karfe 12:00 na tsakar dare zuwa 6:00 na yammacin ranar Asabar 18 ga watan Maris, 2023, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Usman Baba ya ƙara da cewa dokar ba zata yi aiki kan ma'aikatan da ke bauta wa ƙasa a ranar ba kamar jami'an hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, masu sa ido, kafafen watsa labarai da aka tantance, motar Ujila, jami'an kwana-kwana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, haramta zirga-zirga ranar zaɓe ba zata hau kan irin waɗannan ma'aikatan ba domin al'umma suke yi wa aiki da sauran makamantansu.

Bugu da ƙari, IGP ya ce dokar ba zafa shafi babban birnin tarayya Abuja ba saboda babu zaben da za'a gudana ranar.

A rahoton Punch, Adejobi ya ce:

"Baya ga haka, Sufeta janar ya jaddada haramci ga jami'an tsaron da ke tare da manyan mutane da dogarai su raka iyayen gidansu ko 'yan siyasa zuwa rumfunan zabe ko wurin tattara sakamako a ranar zaɓe."

Kara karanta wannan

Jerin 'Yan Takarar Gwamna 3 da Aka Raina Kuma Zasu Iya Ba Da Mamaki a Zaben Gwamnoni

"Haka nan rundunar tsaron da jihohi suka kafa, 'yan sa kai da masu zaman kansu, duk an hana su shiga harkokin zabe a faɗin Najeriya."

IGP Baba ya yi kira da yan Najeriya su zama masu bin doka sau da ƙafa yayin da kuma bayan zaɓe kana ya kara basu tabbacin cewa rundunar ta gama shirin ba su kariya.

Yan bindiga sun sako ɗan takarar LP a Ribas

A wani labarin kuma Dan Takarar LP da Aka Sace Ya Kubuta, Ya Faɗi Abinda Ya Gani Wurin Yan Bindiga

Mai neman kujerar mamba a majalisar dokokin jihar Ribas karkashin inuwar LP, wanda yan bindiga suka yi garkuwa da shi ya shaƙi iskar yanci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel