Asiri Zai Tonu, Shugabannin Jam’iyyar APC Na Fada Kan Zargin Cinye Kudin Kamfe

Asiri Zai Tonu, Shugabannin Jam’iyyar APC Na Fada Kan Zargin Cinye Kudin Kamfe

  • Kalaman Salihu Mohammed Lukman a kan batun batar da kudin kamfe a Osun sun tada kura
  • Sanata Iyiola Omisore ya yi wuf ya maidawa ‘dan majalisarsa ta NWC raddi, ya nuna zai je kotu
  • Sakataren APC ya karyata zargin Mataimakin shugaban jam’iyyar a wata wasika daga Lauyansa

Abuja - Akwai baraka a jam’iyyar APC domin sabani ya shiga tsakanin shugabannin majalisar gudanarwa na NWC, har ana maganar zuwa kotu.

A rahoton Daily Trust na ranar Alhamis, an ji cewa wasu kalamai da suka fito daga bakin Salihu Mohammed Lukman sun jefa shi a cikin matsala.

Salihu Mohammed Lukman wanda shi ne mataimakin shugaban APC na Arewa maso yamma, ya zargi Iyiola Omisore da batar da kudin yakin zabe.

Da aka yi hira da shi a tashar AIT, Lukman ya ce Sakataren jam’iyya na kasa ya yi fatali da kudin da APC ta ware domin ayi kamfe a jiharsa ta Osun.

Kara karanta wannan

Malaman Musulunci Sun ba Tinubu, Zababbun Shugabanni Shawara Kafin Shiga Ofis

A cewar Lukman, Sanata Iyiola Omisore ya ki yi wa kowa bayanin inda kudin suka shiga, yake cewa akwai bukatar a rika yin aiki a APC da gaskiya.

Sanata Iyiola Omisore ya yi martani

Kafin a je ko ina sai aka ji Vanguard ta rahoto cewa tsohon Gwamnan na jihar Osun ya maida martani, ya na kuma yi wa Lukman barazana da kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan APC
Shugabannin Jam'iyyar APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Sakataren jam’iyyar mai mulki a Najeriya ya rubuta wasika ta hannun Lauyansa, Gboyega Oyewole yana zarginsa da kalamai na karya da yaudara.

Oyewole (SAN) yana neman Naira miliyan 500 a hannun ‘dan majalisar ta NWC, tare da haka kuma zai nemi afuwarsa a kafofin labarai, ko a shiga kotu.

A wasikar Lauyan, an tuhumi mataimakin shugaban APC da kalamai na batanci da cin zarafi, wadanda bayan sun kasance na karya, su na bata suna.

Kara karanta wannan

Mukarrabin Jonathan Ya Fadi Yaudarar da Tinubu ya yi Amfani da Ita Wajen Doke Atiku

Takardar ta nuna Omisore yana zargin abokan aikinsa da kokarin ci masa mutunci da jawo masa rashin kima a idanun duniya saboda sabani na siyasa.

Da aka tuntubi wanda ake zargi, ya shaidawa jaridar The Cable cewa zai maida martani lokacin da ya dace, ya ce an yi haka ne saboda a ba shi tsoro.

Wasikar Gwamnan Bauchi

Ana da labari cewa Gwamnan Bauchi ya fadawa Shugaban kasa, Sadiq – Baba Abubakar yana yawo da ‘yan daba a kamfe, hakan ya jawo rasa rayuka.

Kamar yadda Bala Mohammed ya bayyana a wasikarsa, daga cikin garuruwan da ake zargi APC ta jawo rikici akwai Akuyam, Misau, Akuyam da Alkaleri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel