Zaben Gwamnan Jihar Kano: Shin Tarihi Na Shirin Sake Maimaita Kansa Ne

Zaben Gwamnan Jihar Kano: Shin Tarihi Na Shirin Sake Maimaita Kansa Ne

A yayin da zaɓukan gwamnoni ke ƙara tunkarowa a Kano, jam'iyyun adawa na cigaba da nuna yatsa ga gwamnatin APC dake mulkin jihar bisa zarge zarge iri iri.

Gabatowar Zaɓen da za'a yi a 11 ga watan Maris, yasa jam'iyyun adawa ke zargin gwamnatin jihar da gayyato ƴan jagaliyar siyasa daga ƙasashe masu maƙwabtaka da Najeriya domin su kawo wa zaɓen cikas.

Babbar jam'iyyar adawa ta NNPP ce ta zargi gwamnatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje a bisa hayar ƴan jagaliyar siyasa daga ƙasashen waje domin su canja fasalin zaɓen domin yayi mata kyau, rahoton DailyPost.

Gannduje
Zaben Gwamnan Jihar Kano: Kwankwaso Da Ganduje Hoto: Kwankwaso
Asali: Facebook

A cewar NNPP:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Muna sane da wasu yan jagaliyar siyasa dubunnai da aka ɗauko haya daga Chadi, jamhuriyar Niger da kuma Katsina da Kaduna. Waɗannan yan jagaliyar Gwamnatin Gandujiyya ce ta ɗauko su haya domin su lalata zaɓe.

Kara karanta wannan

"Zan Tattauna Da Ƴan Bindiga Idan Aka Zaɓe Ni" Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Kaduna

Jam'iyyar ta ƙara da cewa:

"Dole ne jami'an tsaron farin kaya na DSS da ƴan sandan Najeriya su kula da wannan abin takaicin. Waɗannan yan jagaliyar, suna ɗauke da muggan makamai ne kamar su bindigogi, adduna sannan kuma an jibge su lungu da saƙo na jihar Kano ne wuri wuri a cikin ƙananan hukumomi 44 da muke dasu.

Kiran da jam'iyyar NNPP tayi, ya haɗa da jan hankalin Gwamnatin Tarayya akan abubuwan da za'a iya yi ranar zaɓe daka iya kawo hargitsi.

Inda jam'iyyar tace, duk abinda ya faru a zargi gwamnan jihar Kano Ganduje da kuma shugaban DSS na Kano wanda tun bayan shekara guda data gabata ya kamata ace yayi ritaya.

Jam'iyyar ta ƙara da cewa:

"Jami'an tsaro kamata yayi su dinga fargar daji wajen kare abubuwan da basu da kyau na jihar Kano tun kafin su faru. Inji jawabin na NNPP.

Kara karanta wannan

Muna Jiran Hukuncin Kotun ƙoli Akan Lamarin Shekarau Inji NNPP

Gwamnatin Kano ta Zargi Jam'iyyar NNPP itama

Da yake nashi jawabin, Muhammad Garba wanda yake Kwamashinan labarai na jihar Kano, ya faɗi cewa, akwai rahotanni da suke nuna cewa, abinda NNPP take faɗa, shine abinda ita NNPP din take shirin aikawata "kamar yadda sukayi a zaɓen daya wuce na shugaban ƙasa".

Garba yace, NNPP sun fahimci cewa an gano manaƙisar da suke ƙullawa ne, yasa suka maida Martani da hakan, Legit ta ruwaito.

Ya ce:

"NNPP sun san cewa, ba zasu yi nasara bane, shi yasa suka fito da wannan dabarar. Inji Garba.

Muhammad Garba kuma ya zargi NNPP da tunzura matasa suna ƙin yiwa iyayen su biyayya.

Inda ya bada dalili na hujja da yadda ake dinga rasa rayuka a gangamin da NNPP tayi na neman zaɓe.

Muhammad Garba yace:

"Jam'iyyar APC jam'iyya ce mai son zaman lafiya, kuma zasu bawa jami'an tsaro duk gudunmawa da suke buƙata wajen tabbatar da zaɓe mai cike da sahihanci da zaman lafiya a jihar". Inji mai magana da yawun gwamnatin.

Kara karanta wannan

Ana Dab Da Zaɓen Gwamnoni, Jam'iyyar Labour Party Ta Bayar Da Wani Muhimmin Umurni Ga Magoya Bayanta

Zarge Zarge Na Ƙara Ƙamari

Shima ɗan Takarar Jam'iyyar ADC na gwamnan, Ibrahim Khalil, ya zargi gwamnatin ta Kano a wata hira da manema labarai da yayi na cewar wasu yan siyasa marasa kishi sun ɗauki marasa tarbiyya haya domin lalata yadda zaɓe zai kasance idan an soma, rahoton Premium Times.

A cewar Ibrahim Khalil:

"Rahoto yazo mana cewar, wasu ƴan siyasa marasa kishi sun ɗauko ƴan jagaliyar siyasa domin lalata zaɓen da za'a yi.
"Kuma mun samu rahoton cewa, za'a bawa yan jagaliya kayan jami'an tsaro a zaɓen gwamnan da zaizo na 11 ga watan Maris na 2023.

Ibrahim Khalil yayi kira ga jami'an tsaro, Kungiyoyi na Duniya, ƙasashen waje, masu saka ido, masu rajin kare hakkin dan adam, yan jaridu, da uwa uba INEC wajen ganin sunyi abinda ya dace domin samun dawwamammen zaman lafiya mai ɗaurewa yayi da bayan gudanar da zaɓen.

Sannan yayi kira ga INEC data kai kayan zaɓe akan lokaci. Saboda yayi nuni da cewar, akwai tunanin da ake na shirin maguɗi naƙin kai kayan zaɓe akan lokaci. Musamman a Kano ta tsakiya, inda yace zaɓe ba wani abu bane na ko a mutu ko ayi rai.

Kara karanta wannan

"Ba Zamu Yarda NNPP ta Haddasa Mana Rikici a Zaɓe Mai Zuwa Ba" - Gwamnatin Kano

Yan takarkarun da suka haɗu suka sahale sakon na Ibrahim Khalil sun haɗa da Bala Gwagwarwa (SDP), Sadiq Wali, (PDP) da Tanko Yakasai (PRP).

Sauran sun haɗa da Yakubu Uba-Gaya (YPP), Ibrahim Muhammad (APP), Aisha Mahmud (NRM), Furera Ahmad (BP) da kuma Sha’aban Ibrahim Sharada (ADP).

Abinda ya faru ranar zaben shugaban kasa Feb 25

A ranar zaben shugaban kasa, an samu tashin hankula a wurare daban-daban musamman karamar hukumar Tudun-wada inda hukumar yan sanda ta bayyana cewa an kona wasu yan jam'iyyar NNPP da ransu.

Daily Trust ta ruwaito kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Abdullahi Kiyawa, da cewa akalla mutum biyu aka kona cikin ofishin kamfen NNPP.

Haka Legit ta koro labarin yadda aka bankawa ofishin NNPP wuta.

Tuni dai an gurfanar da dan majalisa mai wakiltar mazabar Doguwa da Tudun wada bisa zargin hannu cikin wadannan kashe-kashe.

Hakazalika an damke zababben dan majalisar NNPP, Madakin Gini, bisa rike bindiga ba tare sahalewar hukuma ba.

Kara karanta wannan

Zaɓen Gwamnoni: NNPP Tayi Gargaɗi Mai Zafi Kan Shugabannin Ta Da Mambobin Ta

Abinda ya faru a 2019

Zaku tuna cewa a zaben gwamnan jihar Kano ta 2019 tsakanin Abba Kabir Yusuf da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, an samu tarzoma inda abin ya kai ga manya suka sanya baki.

Gwamna Ganduje ya samu nasara a zaben bayan zagaye na biyu da akayi inda ya samu galaba.

Wannan zabe wanda darikar Kwankwasiyya tace an tafka magudi kuma an kwace mulki karfi da yaji ke sabbaba zarge-zargen da ake yanzu.

Zanga-zanga kullum

Cikin kwanaki biyu da suka gabata, mamabobin jam'iyyar NNPP sun gudanar da zanga-zanga kan wani jami'in hukumar yan sanda da kuma Sakataren hukumar INEC na jihar.

Yayinda suka ce basu amince a turo CP Balarabe Sule ba saboda suna zargin zai hada kai da gwamnatin Kano, sun bukaci a sallami Sakataren INEC, Garba Lawan, kafin ranar zabe.

Hukumar Ƴan Sanda Ta Magantu

A wani tsagin kuma, ana tsaka da haka ne, kakakin hukumar ƴan sanda ta jihar Kano, ta bakin SP Haruna Kiyawa ta magantu akan balahirar.

Kara karanta wannan

An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC a Neja Bisa Zargin Dangwalawa Atiku Kuri'a

"Hukumar yan sanda ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan yan sanda CP Mamman Dauda PSC, ta amshi bayanan sirri dake nuna yadda yan siyasa marasa kishi zasu aikata ba daidai ba wajen zaben gwamna dana majalisar jiha a ranar 11 ga Maris na 2023.
"Kwamishinan yan sanda yana gargaɗi ga duk wani ɓata gari dake jihar dasu kuka da kansu su fice, saboda bazamuyi wata wata ba wajen ladabtar dasu".

Sannan Kiyawa ya ƙara da cewa, hukumar zata haɗa kai da sauran hukumomin tsaro na jihar wajen kama masu laifi tare da kaisu kotu domin girbar abinda suka shuka.

Ya ƙarƙare da godiya ga mutane suka bi doka da oda a zaɓukan da suka gabata na shugaban ƙasa da Sanatoci. Sannan ya bada lambar waya 08032419754, 08123821575, ko 0902929292.

Asali: Legit.ng

Online view pixel