APCPDP: An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC na Niger Saboda Dangwalawa Atiku Kuri'a da Yayi.

APCPDP: An Dakatar da Shugaban Jam'iyyar APC na Niger Saboda Dangwalawa Atiku Kuri'a da Yayi.

  • An fittiki shugaban jam'iyya sukutum bisa zargin ya dangwalawa dan takarar jam'iyyar adawa kuri'a
  • An zargi shugaban jam'iyyar da yin amfani da kudin APC wajen yakin ganin Atiku ya zama Shugaban Kasar
  • Mambobin kwamitin gudanarwa ta jihar Neja ta dakatad da shugaban APC na yankin Agwara

Batu ake na tsallake gida tare da zuwa maƙwabta yin biki irin na siyasa da wani shugaba jam'iyyar APC yayi na tsalllen baɗake daga jam'iyyar sa zuwa jam'iyyar PDP domin saka musu ƙuri'a.

Jam'iyyar APC
Jam'iyyar APC na Niger
Asali: Twitter

Ko me yayi zafi?

Shi dai Haliru Zakari Jikan Toro shine shugaban jam'iyyar APC na Agwara wanda aka sallama saboda ayyukan da suka jiɓanci anti party da yiwa jam'iyya zagon ƙasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Abin Ban Takaici Cocin Gidan Gwamnati Ta Aso Rock Za'a Rufe ta Na Tsawon Shekara 4 - Okowa

A wata wasiƙa da aka aika a 2 ga watan Maris wacce Sakataren Mazaɓar Kashini dake Ƙaramar Hukumar Agwara , wato Amadu Abdullahi Yagode da Nurudeen Abdullahi suka sahale haɗe da mutane 21 masu faɗa aji a mazaɓar.

Sun amince tare da dakatarwar da aka yi wa shugaban jam'iyyar biyo bayan zargin da akayi masa na dangwalawa jam'iyyar PDP kuri'a sannan kuma yayi musu yaƙin ganin sun samu nasara a akwatunan dake mazaɓar.

Idan za'a iya tunawa, Atiku Abubakar shine ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP a zaɓen daya gabata.

Daily Trust ta ruwaito wasiƙar da aka dakatar dashi tana cewa:

"Wannan dakatarwa da akayi maka tana zuwa ne sakamakon saɓawa gamida nuna halin ko in kula dakayi wa jam'iyyar mu ta APC. Ayyukan da kayi na ranar zaɓen, Honorabul Haliru Zakari Jikantoro, ya taimaka mana wajen rashin samun nasara a zaɓen daya wuce na shugaban ƙasa dana ƴan majalisun 2023 a ranar 25 ga watan Fabrairu na 2023".

Kara karanta wannan

Goyon Bayan Tinubu: Ɗan Takarar Gwamnan Labour Party Na Ruwa, Jam'iyyar Na Shirin Juya Masa Baya

"Akan haka ne, yakai Hon. Haliru Zakari Jikantoro muke kamaka da yin ayyukan zagon ƙasa ga jam'iyyar mu ta Hanyar taimakawa PDP."

Bayanin Wasiƙar kuma ya zargi Hon. Haliru Zakari Jikantoro da ƙin kiran taron jam'iyya tare da yin duk wani shiri mai muhimmanci a lokacin da zaɓen yake ƙaratowa.

Bugu da ƙari, jam'iyyar tayi mamaki akan yadda Hon Haliru Zakari Jikantoro yayi amfani da kuɗin jam'iyyar APC wajen yiwa jam'iyyar PDP yaƙin neman zaɓe.

Wasiƙar ta ƙarƙare da cewa:

"Bugu da Ƙari, lokacin zaɓen gama gari na 25 ga watan Fabrairu na 2023 , mun gani cewa mazaɓar Hon Haliru Zakari Jikantoro a firamaren Kashini, Agwara, ya zaɓi PDP ne tare da tattarawa PDP kuri'a, dalili da yasa jam'iyyar mu ta gaza kawo akwatin da yake zaɓe a ciki."

Duk wani ƙoƙari da majiyar mu tayi domin jin martanin sa game da wannan wasikar da yasamu, abin yaci tura, domin Hon Haliru Zakari Jikantoro baya ɗaukan waya, ballantana dawo da gajeren saƙon da aka aika masa har zuwa lokacin da muke kammala haɗa rahoton nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon Gwamnan Ekiti Fayose, Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP

Abin Ban Takaici Cocin Gidan Gwamnati Ta Asoroko Za'a Rufe ta Na Tsawon Shekara 4 - Okowa

Gwamnan jihar Delta, kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP daya sha kayi a zaɓen daya wuce.

Yayi korafi a kan cewa, ba haka aka so ba ace wai za'a kulle babbar cocin dake cikin fadar shugaban kasa ta Ado Rock saboda tikitin da APC ta bayar na musulmi da Musulmi a zaɓen daya gabata.

Okowa yayi wannan batu ne a wani taro da yayi da ilahirin shugabancin wata babbar coci mai suna "God's Fountain of Life Mission" a gundumar Oleh dake ƙaramar hukumar Isoko South ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel