Bai Kamata Obaseki Ya Damu da Batun Tunbuke Shi Daga Kujerar Gwamna Ba, Oshiomhole

Bai Kamata Obaseki Ya Damu da Batun Tunbuke Shi Daga Kujerar Gwamna Ba, Oshiomhole

  • A ranar 11 ga watan Maris, 2023 za'a gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya kuma tuni INEC ta yi nisa a shirye-shiryenta
  • Yayin da wasu gwamnoni ke fafutukar tazarce a kan kujerunsu, wasu kuma tuni suka san makomarsu saboda rashin katabus a zangon mulkinsu
  • Abin sha'awar, tsohon gwamnan Edo, Adama Oshiomhole, ya bukaci gwamna Godwin Obaseki ya kwantar da hankalinsa kar ya sa damuwa a ransa

Edo - Gabanin ranar Asabar 11 ga watan Maris, 2023 da za'a gudanar da zaben mambobin majlisar dokoki, tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole, ya aike da sako ga magajinsa.

Kwamaret Oshiomhole ya ce bai kamata wanda ya gaje shi, gwamna Godwin Obaseki, ya damu da batun tsige shi daga kan kujerarsa ba idan jam'iyyarsa ta yi rashin nasara.

Gwamna Obaseki da Oshiomhole.
Tsohon shugaban APC ya aike da sako ga gwamna Obaseki Hoto: channelstv
Asali: UGC

Tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya yi wannan furuci ne yayin hira da manema labarai a Benin City, babban birnin jihar Edo, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana Kishin-Kishin Wani Gwamna APC Zai Baiwa Duk Wanda Ya Zaɓe Shi N20,000, Gaskiya Ta Fito

Legit.ng Hausa ta gano cewa Oshiomhole ya lashe kujerar Sanata mai wakiltar mazabar Edo ta arewa a majalisar Dattawa a zaben ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jigon APC ya aika sako ga Obaseki

Tsohon gwamnan ya jaddada cewa idan har Obaseki ya yi aikin da mutane ke bukata a matsayin gwamnan Edo, bai kamata ya damu ba idan masu kada kuri'u sun ƙaurace wa PDP.

Ya kuma zargi gwamnatin Obaseki da rashin sakar wa bangaren masu yin doka mara su yi aikin da kundin mulki ya ɗora masu ba.

"Maƙasudin kafa majalisar dokoki shi ne su tantance duk wani yunkurin ɓangaren zartaswa a dokance, ba wai haka nan zasu kashe miliyoyi ba, ko ma na ce biliyoyi, dole sai an bi ta ɓangaren doka."

A cewarsa, 'yan takarar majalisar dokokin, "Sun ƙagara su tabbatar da cewa gwamna ya kashe arzikin jihar ta hanyar da mutanen mazabu suke muradi, tsige shi ba ya cikin manufofin su."

Kara karanta wannan

Kwana 7 Gabanin Zaben Gwamnoni, Hadimin Gwamnan APC Ya Yi Murabus, Ya Koma PDP

APC ta kara karfi a Gombe

A wani labarin kuma Ana dab da zaben gwamna, babban jigon siyasa da mambobi sama da 5000 sun sauya sheƙa zuwa APC

Muhammad Isa, jigon jam'iyyar ADC ya tattara magoya bayansa, ya ce sun hango kyaun goben Gombawa a karkashin mulkin gwamna Muhammad Inuwa.

Gwamna Inuwa ya musu maraba kana ya sake rokon mutane da su sake baiwa gwamnatinsa dama a karo na biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel