Ban da Alaka da Garabasar N20,000 Ga Duk Wanda Ya Zabi Abiodun, Gwamnan Ogun

Ban da Alaka da Garabasar N20,000 Ga Duk Wanda Ya Zabi Abiodun, Gwamnan Ogun

  • Gwamnan jihar Ogun ya nesanta kansa da wani kamfe na garabasar kuɗi har N20,000 ga duk wanda ya zaɓi APC ranar Asabar
  • Ta hannun sakataren watsa labaransa, gwamnan ya ce abokan karawarsa ne suka kirkiri lamarin domin rage masa farin jini
  • A cewar sanarwan, gwamna Abiodun ba zai ba kuma ba zai taimaka a riƙa sayen kuri'u ba, ya maida hankali wurin tallata kansa da ayyuka da ya yi

Ogun - Gwamnatin jihar Ogun ta nesanta kanta da "Garabasar kamfen Dapo Abiodun N20,000" da ake ci gaba da yaɗawa a kafafen sada zumunta, kamar yadda Punch ta rahoto.

Sakataren watsa labarai na ofishin gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun, Kunle Somorin, a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, ya ce gwamnatin jihar ba ta da hannu a garabasar.

Kara karanta wannan

Abin Ban Takaici Cocin Gidan Gwamnati Ta Aso Rock Za'a Rufe ta Na Tsawon Shekara 4 - Okowa

Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun.
Ban da Alaka da Garabasar N20,000 Ga Duk Wanda Ya Zabi Abiodun, Gwamnan Ogun Hoto: Dapo Abiodun
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa kamfen wani yunkuri ne na yaudarar mutane da kuma ɓata wa gwamna suna yayin da ake tunkarar zaben gwamnoni ranar Asabar mai zuwa 11 ga watan Maris, 2023.

Ya ƙara da cewa abokan karawar gwamna Abiodun ne suka kirkiro wannan shirin garabasar bayan sun fahimci cewa ba zasu iya kayar da shi ba idan aka fafata zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwan ta wanke mai girma gwamnan Ogun da cewa Abiodun ba zai taɓa taimaka wa wajen sayen kuri'u ba kai tsaye ko ta bayan fage ba zai taba yin haka ba.

Haka zalika ta yi bayanin cewa gwamna Abidoun ba zai taba amfani da kyayyakin amfanin yau da kullum ba wajen jan hankalin masu kaɗa kuri'a su zaɓe shi.

A rahoton The Nation, Wani bangaren sanarwan ya ce:

"Maimakon haka gwamna Abiodun ya maida hankali wurin kamfen baje kolin ayyukansa, kaddamar da manyan ayyukan raya kasa da jan hankalin mutane su zaɓi APC."

Kara karanta wannan

2023: "Ban San Komai Ba" Atiku Ya Maida Martani Kan Yunkurin Tinubu Na Neman Sulhu

Jam'iyyar PDP Ta Karyata Jita-Jitar Gwamna Adeleke Zai Koma APC

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Osun ta musanta raɗe-radin cewa gwamna ya kammala shirin sauya sheƙa

A wata sanarwa da shugaban jam'iyyar na jiha ya fitar, ya ce APC ta kirkiro labarin domin ta ɗauke wa mutane hankali bayan kunyar da ta sha ranar zaben shugaban kasa.

A cewarsa, gwamna Adeleke na nan daram a PDP kuma ya shirya tsaf wajen sake kawo wa jam'iyyar nasara a zabe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel