Hadimin Gwamnan APC Ya Yi Murabus Kwana 7 Gabanin Zaben Gwamnoni

Hadimin Gwamnan APC Ya Yi Murabus Kwana 7 Gabanin Zaben Gwamnoni

  • Hadimin gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya yi murabus daga muƙaminsa, ya sauya sheka zuwa jam'iyar PDP
  • Honorabul Mark Onu, ya tabbatar da matakin da ya ɗauka ranar Jumu'a kana ya ayyana goyon baya ga Ifeanyi Chukwuma Odii
  • Ya ce zai ba da gudummuwa iya karfinsa wajen ganin ɗan takarar PDP ya samu nasarar zama gwamna a zaben Asabar mai zuwa

Ebonyi - Mai baiwa gwamna David Umahi Shawara ta musamman kan harkokin matasa da safarar kwayoyi, Honorabul Mark Onu, ya yi murabus daga muƙaminsa ranar Jumu'a.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa bayan Murabus daga majalisar zataswa, tsohon hadimin gwamnan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi.
Gwamna Umahi yana jawabi a Ofis Hoto: Dave Umahi
Asali: UGC

Mista Onu, wanda aka fi sani da "Chopper" ya ayyana goyon bayan ga ɗan takarar gwamnan Ebonyi karkashin inuwar PDP, Ifeanyi Chukwuma Odii, a zaben 11 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Bayan Tinubu Ya Ci Zaɓe, Babban Jigon PDP Ya Jingine Tafiyar Atiku, Ya Koma Jam'iyyar APC

Tsohon hadimin gwamnan ya faɗi haka ne yayin hira da 'yan jarida a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi, inda ya tabbatar da cewa ya koma gidan da ya hito wato PDP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan ya shaida wa ɗumbin masoyansa musamman matasa cewa ya zama tilas ya koma PDP saboda Dakta Ifeanyi Odii ne mafi alkairi ga mutanen Ebonyi idan ya zama gwamna.

A kalamansa, Mista Onu ya ce:

"Dukkan mu mun san waye Anyi Chuks, kuma ina ganin ruhina ba zai taɓa yafe mun ba idan har ban koma inuwar masu kishin Ebonyi ba domin kawo adalci da labari mai daɗi ga Ndi Ebonyi."

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa Honorabul Onu na ɗaya daga cikin manyan kusoshin gwamnatin gwamna Umahi, wadanda suka sadaukar da aikinsu domin komawa PDP.

Sun yi haka ne domin ba gudummuwa wajen ganin Dakta Odii ya kai ga nasarar zama zababben gwamnan Ebonyi a zaben ranar 11 ga watan Maris, 2023, kamar yadda Independent ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsohon Gwamnan Ekiti Fayose, Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP

An bukaci INEC ta fito ta yi bayani dalla-dalla

A wani labarin kuma Tsoffin Gwamnoni da Ministoci, Sanatoci da Wasu Manya Sun Huro Wa INEC Wuta

Ƙungiyar haɗa kan ƙasa da tabbatar da zaman lafiya ta nemi hukumar zabe ta yi karin haske kan gazawarta na ɗora sakamakon zaben a shafin intanet.

Kungiyar, wacce ta kunshi tsofafffin gwamnoni da Ministoci, Sanatoci da yan majalisun tarayya, ta ce ya kamata INEC ta ɗauki mataki kafin zaben gwamnoni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel