Jam'iyyar APC Ta Karbi Dubbannin Masu Sauya Sheka a Jihar Gombe

Jam'iyyar APC Ta Karbi Dubbannin Masu Sauya Sheka a Jihar Gombe

  • Kwanaki 6 gabanin zaben gwamna, APC mai mulkin Gombe ta gamu da gagarumin goyon baya a yankin Dogon Ruwa
  • Wani babban ɗan siyasa da magoya bayansa akalla 5000 sun tattara kayansu sun koma inuwar APC
  • Da ya ke maraba da masu sauya sheƙar, gwamna Yahaya ya roki mazauna jihar su ci gaba da amince wa da APC a zabe mai zuwa

Gombe - All Progressives Congress watau APC a mazaɓar Dogon Ruwa, ƙaramar hukumar Kaltungo a jihar Gombe ta samu gagarumin ƙarin goyon baya.

Punch ta rahoto cewa 'yan siyasa akalla 5,000 ne suka sauya sheka zuwa APC a yankin yayin da ya rage kwanaki 6 gabanin zaɓen gwamna da mambobin majalisar dokoki.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya.
Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya a wurin kamfe Hoto: Inuwa Yahaya
Asali: Facebook

Bayanai sun nuna cewa wannan ci gaban ya biyo bayan sauya shekar babban jigon siyasa, Muhammad Isa, tare da magoya bayansa daga jam'iyyar ADC zuwa APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Babbar Nasara: 'Yan Ta'adda Sama da 1,000 Tare da Iyalansu Sun Tuba Sun Miƙa Wuya a Arewacin Najeriya

Da yake maraba da dubbannin masu sauya sheƙar a Dogon Ruwa, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ya roki masu kaɗa kuri'u su ci gaba da amince wa APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatinsa, Farfesa Ibrahim Njodi, ya bukaci mazauna Gombe su kara sahalewa APC ta hanyar sake miƙa amanarsu ga gwamnati mai ci.

Ya ce:

"Mun yi abin a yaba a ɓangaren walwala da tattalin arziki da kuma raya ayyukan ci gaban ƙasa cikin shekaru uku da rabi da suka gabata."

Meyasa Jigon da magoya bayansa suka koma APC?

A nasa jawabin tun da farko, babban jigo a cikin masu sauya shekar, Mista Isa, ya ce ya ɗauki matakin shiga APC tare da magoya bayansa ne saboda ganin kokarin gwamnatin Inuwa Yahaya.

Haka zalika mamba mai wakiltar gabashin Kaltungo a majalisar dokokin jihar, Yerima Gaule, ya tabbatar wa gwamnan zai samu nasara a mazaɓarsa, Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kwana 7 Gabanin Zaben Gwamnoni, Hadimin Gwamnan APC Ya Yi Murabus, Ya Koma PDP

A wani labarin kuma Kungiyoyin Magoya Bayan Tinubu Sun Goyi Bayan Tazarcen Gwamnan PDP

Yayin da ake tunkarar zaben gwamnoni ranar Asabar mai zuwa, kungiyoyin magoya bayan Tinubu sun lashi takobin saka alkairin da aka masu a Oyo.

Gamayyar kungiyoyin sun sha alwashin yin aiki don tabbatar da nasarar gwamna Seyi Makinde, wanda ke neman tazarce karkashin PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel