Jam'iyyar Labour Party Ta Caccaki Ɗan Takarar Gwamnan Ta Na Adamawa

Jam'iyyar Labour Party Ta Caccaki Ɗan Takarar Gwamnan Ta Na Adamawa

  • Jam'iyyar Labour Party a jihar Adamawa, ta caccaki ɗan takarar gwamnan ta bisa goyon bayan Tinubu
  • Ɗan takarar gwamnan dai ya fito fili ya nuna goyon bayan sa ga Tinubu a maimakon Peter Obi
  • Jam'iyyar na shirin yi masa hukunci inda ta ƙi cewa magoya bayan ta da su zaɓe shi a zaɓen gwamnan da za a yi

Jihar Adamawa- Jam'iyyar Labour Party (LP) a jihar Adamawa, ta caccaki ɗan takarar gwamnan ta, Umaru Mustapha, bisa zargin sa da cewa magoya bayan sa su zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu.

Shugaban jam'iyyar na jihar Adamawa, Christopher Nicolas, a wajen wani taro da manema labarai a ranar Alhamis, ya bayyana cewa Mustapha ya gayawa magoya bayan su su zaɓi Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa. Rahoton The Cable

Kara karanta wannan

Atiku Yayi Magana Kan Peter Obi, Ya Bayyana Babban Naƙasun Da Ya Yiwa PDP

Labour Party
Jam'iyyar Labour Party Ta Caccaki Ɗan Takarar Gwamnan Ta Na Adamawa Hoto: Ripples Nigeria
Asali: UGC

Shugaban jam'iyyar ya kuma nuna godiyar sa kan magoya bayan jam'iyyar bisa yadda suka fito suka ƙadawa Peter Obi, ƙuri'u a ranar zaɓen shugaban ƙasa.

Ya kuma yi kira ga magoya bayan jam'iyyar da su zaɓi ƴan takarar jam'iyyar dake takara a matakin neman kujerun majalisar jihar. Rahoton Vanguard

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A madadin shugaban mu, shugaban jam'iyya na ƙasa, muna godiya ga magoya bayan mu kan ƙuri'un da suka bamu. Mun gode muku sosai." A cewar sa
“Sannan muna roƙon ku da ku zaɓi ƴan takarar jam'iyyar mu dake takarar kujerun majalisar jiha."
“Sai dai a kujerar gwamna, muna aiki akai tukunna saboda ya fito fili ya juyawa shugaban mu baya, sannan ya nemi magoya bayan sa da su zaɓi jam'iyyar APC, wanda hakan babban laifi ne a wajen mu."

Gwamnan Jihar Katsina Ya Sake Korar Wani Jami'in Gwamnatin Sa

Kara karanta wannan

Shugaban APC Na Ƙasa Ya Caccaki PDP Da LP, Ya Tono Wata Maƙarƙashiyar Da Suke Ƙullawa

A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya cigaba da korar jami'an gwamnatin sa. Gwamnan yayi kora sosai tun bayan zaɓen shugaban ƙasa da aka yi.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, bai samu nasara ba a jihar Katsina, inda jam'iyyar APC ke mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel