Gwamnan Jihar Katsina Ya Sake Korar Wani Jami'in Gwamnatin Sa

Gwamnan Jihar Katsina Ya Sake Korar Wani Jami'in Gwamnatin Sa

  • Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sake korar wani daga cikin muƙarraban gwamnatin sa
  • Gwamnan dai ya kori jami'an gwamnatin sa da dama tun bayan da jam'iyyar APC ta faɗi zaɓen shugaban ƙasa a jihar
  • Sakataren gwamnatin jihar ya bayyana dalilin gwamna Masari na yin korar da yake yi

Jihar Katsina- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya kori shugaban hukumar sufuri ta jihar, (KSTA), Alhaji Bilyaminu Mohammed-Rimi, daga muƙamin sa.

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Muntari Lawal, shine ya bayyana hakan a ranar Alhamis a birnin Katsina. Rahoton Daily Trust

Masari
Gwamnan Jihar Katsina Ya Sake Korar Wani Jami'in Gwamnatin Sa Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Muntari Lawal yace korar da aka yiwa shugaban hukumar sufurin ta fara aiki nan take.

Sakataren gwamnatin ya kuma ƙara da cewa gwamna Masari, ya naɗa Alhaji Gambo Abdulkadir-Rimi, a matsayin sabon shugaban hukumar ta KTSTA.

Kara karanta wannan

"Shi Ne Daidai" Gwamna Masari Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Bayan Tinubu Ya Ci Zaɓe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masari ya kuma ƙori Alhaji Tasi’u Dahiru-Dandagoro, kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar a ranar Litinin.

Ya kuma kori sakatariyar hukumar cimma muradun ƙarni Hajia Fatima Ahmed; sakataren minisitan noma da albarkatun ƙasa, Alhaji Aminu Waziri; da shugaban hukumar jindaɗin Alhazai ta jihar Alhaji Yusuf Barmo.

Alhaji Muntari Lawal ya bayyana cewa korar da gwamnan ya yi musu, wani ɓangare ne na yin garambawul ga gwamnatin sa.

Wata majiya mai tushe daga gidan gwamnatin jihar, tayi nuni da cewa korar da gwamnan jihar yake yi, bata rasa nasaba da shan kayen da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, yayi a jihar.

Tinubu, wanda ya samu ƙuri'u 482,283, yayi rashin nasara a hannun ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar People’s Democratic Party, Atiku Abubakar, wanda ya samu ƙuri'u 489,045 daga ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina. Rahoton Sun

Kara karanta wannan

Masari Ya Shiga Sallamar Masu Rike da Mukamai Tun da Aka Kunyata Tinubu a Katsina

An Dakatar da Shugaban APC a Jihar Neja Saboda Ya Kadawa Atiku Kuri’a

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Neja ta dakatar da shugaban ta saboda ya kadawa Atiku Abubakar ƙuri'a a zaɓen shugaban ƙasa.

Tuni dai jam'iyyar ta aikewa shugaban takardar dakatarwa daga muƙamin sa, saboda wannan abin da yayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel