Tinubu ya Haskawa Atiku Abubuwa 3 da Suka Yi Sanadiyyar Faduwarsa Takara na 6

Tinubu ya Haskawa Atiku Abubuwa 3 da Suka Yi Sanadiyyar Faduwarsa Takara na 6

  • Bola Tinubu ya ce Atiku Abubakar yana shure-shure ne da sunan zai kai kara zuwa kotu zabe
  • Zababben shugaban kasar ya yi magana ta hannun kwamitin yakin takaran APC na zaben 2023
  • Festus Keyamo ya jero wasu abubuwa da yake gani sun taimaka wajen faduwar Wazirin Adamawa

Abuja - Kakakin kwamitin takaran APC na zaben shugaban kasa, Festus Keyamo, ya yi wa Atiku Abubakar shakiyanci bayan ya sake fadi takara.

A ranar Alhamis, Vanguard ta rahoto Festus Keyamo SAN yana cewa tun da Atiku Abubakar ba zai iya samun mulki ba, to kyau ya koma Dubai.

Ministan kasar ya fitar da jawabi da ya caccaki ‘dan takaran PDP, yana mai zarginsa da kashe jam’iyya, ya ce Atiku ya girbi abin da ya shuka ne.

Keyamo yake cewa ya kamata Wazirin Adamawa ya daina yaudarar kansa a kan zabe, hakan martani ne bayan ‘dan takaran ya ce zai je kotu.

Kara karanta wannan

Sakamakon Zaben 2023: Atiku Ya Bayyana Matakin Karshe Da Zai Dauka Idan Bai Yi Nasara A Kotu Ba

Inda PDP ta fadi zaben 2023

Kakakin kwamitin yakin zaben Bola Tinubu ya yi wa ‘dan takaran PDP raddi, ya ce tun asali ya fadi zabe ne da ‘Yan PDP suka shiga LP da NNPP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ra’ayin Keyamo, tsayawa takarar Peter Obi da Dr Rabiu Kwankwaso ya hana PDP samun nasara.

Tinubu
Bola Tinubu da Buhari a Legas Hoto: @Officialasiwajubat
Asali: Facebook

Bugu da kari, Karamin Ministan kwadagon ya ce watsi da tsarin karba-karba da aka yi a PDP, aka tsaida ‘Dan Arewa ya taimaka Atiku ya sha kashi.

Jawabin ya ce bayan Atiku Abubakar ya samu tikitin takara, ya murkushe yankin Kudancin Najeriya, ya ki bari a canza shugaban jam’iyyar PDP.

'A tattara a koma kasar UAE' - APC PCC

Muddin Alhaji Atiku Abubakar ba zai karbi tayin da Bola Tinubu ya yi masa na kafa gwamnatin hadaka ba, Keyamo ya ce ‘Dan siyasar ya koma Dubai.

Kara karanta wannan

Tsakanin Atiku da Obi, Akwai Mai Karyar Shi Ya Lashe Zabe – Tsohon Shugaban APC

This Day ta ce kwamitin neman zaben APC yana ganin tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi namijin kokari da ya iya zuwa na biyu a zaben.

Tinubu ta bakin lauyan ya ce abokin karawarsa yana shure-shure ne da ba zai hana sa mutuwa ba.

Zababben shugaban kasa bai gamsu da zargin da Atiku yake yi na cewa an yi magudi a zaben shugaban kasa ba, ya ce babu wata hujja da ta nuna hakan.

Yaran manya a zaben 2023

Ku na da labari Mai dakin Ministan harkoki na musamman ta yi nasara a kan ‘Dan majalisar PDP a Benuwai, sannan yaron Jerry Gana ya lashe zabe a Neja.

Yaron Gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai ya kawo karshen tazarcen Samaila Suleiman, amma a Kanom Abba Ganduje ba zai tafi Majalisar tarayya ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel