Bincike Ya Fallasa Jihohi 2 da Ake Zargin An Tafka Murdiya a Zaben Shugaban Kasa

Bincike Ya Fallasa Jihohi 2 da Ake Zargin An Tafka Murdiya a Zaben Shugaban Kasa

  • Yiaga Africa ba ta yarda da kuri’un da Hukumar INEC ta ce sun fito daga Jihohin Imo da Ribas a 2023 ba
  • Hasashen da jami’an kungiyar suka gudanar ya nuna sakamakon da aka sanar ya ci karo da abin da ake sa rai
  • Jam’iyyar APC ta samu kuri’un da suka ba jama’a mamaki a jihar Ribas da PDP ta fi yin mulki tun daga 1999

Abuja - Yiaga Africa wata kungiya ce mai zaman kanta, hasashen da tayi game da zaben shugaban kasa bai zo daidai da sanarwar da aka bada ba.

A ranar Alhamis, The Cable ta rahoto Yiaga Africa ta ce akwai alamun da ke nuna an yi coge wajen tattara sakamakon zaben shugaban Najeriya.

Kungiyar ta ce sakamakon da aka tattara a matakin jihohi da mazabu daga Imo da Ribas ba su zo daidai da hasashe na WTV da ta gudanar ba.

Kara karanta wannan

Adadin Kujerun Majalisan Da APC, PDP, NNPP, Da Sauran Jam'iyyu Suka Samu

“A jihar Ribas, INEC ta bada sanarwar APC ta samu kuri’u 231, 591 ko 44.2%; sai LP ta samu 175,071 ko 33.4%; PDP ta samu 88,468 ko 16.9%.
Wannan ya ci karo da hasashen Yiaga Africa WTV na Ribas wanda ya zo; APC 21.7%±5.0 %; sai LP 50.8%±10.6%, sannan PDP 22.2%±6.5%.
A jihar Imo, INEC ta bada sanarwar kuri’u 66,406 ga APC ko 14.2%; sai LP ta samu 360,495 ko 77.1%; sai kuri'u 30,234 ga PDP ko kuma 6.5%.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban Kasan gobe
Bola Tinubu ya samu shaidar zama Shugaban Kasa Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook
A nan ma wannan ya ci karo da hasahen Yiaga Africa WTV na Imo wanda yake: APC 5.1% ±2.3%; LP 88.1% ±3.8% da kuma PDP 5.7%±2.3%.

- Kungiyar YIAGA

Rahoton ya ce binciken da kungiyar ta gudanar ya nuna mata APC za ta tashi da tsakanin 34.4% zuwa 37.4% na kuri’un da aka kada a jihar Imo.

Kara karanta wannan

Hasashen Zaben Gwamna: PDP Zata Lashe Jihohi 15, APC Zata Lashe 10

Jam’iyyar LP za ta tashi da 24.2% zuwa 28.4% na kuri’un, sai PDP ta kare da 28.3% zuwa 31.1%.

Kira ga INEC a zabe mai zuwa

A cikin shawarar da YIAGA ta ba hukumar INEC shi ne a fayyacewa jama’a gaskiyar haka-da-haka da aka samu a zaben da aka yi a Ribas da kuma Imo.

Sannan kungiyar ta bada shawara a zabe mai zuwa, a kara lokacin yin zabe zuwa karfe 5:00 na yamma, sannan a rika daura sakamakon zabuka a IReV.

Janar Babangida ya yi kira ga al’umma

An samu labari cewa Ibrahim Badamasi Babangida ya yi magana a game da sakamakon zaben sabon shugaban kasa, kuma ya yabi aikin hukumar INEC.

Ibrahim Badamasi Babangida ya ce Tinubu yana da duk abin da ake bukata domin kawo cigaba, , a cewarsa zababben shugaban kasar zai iya gyara Najeriya.

Kara karanta wannan

Hukunci 6 da Kotun Koli ta Zartar Game da Tsarin Canza Takardun Kudi a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel